Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,289. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙadamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,309 da raba miliyan 1.2 da muhallansu.

Kai-tsaye: Sabbin hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza sun kashe Falasɗinawa aƙalla 29

Talata, 15 ga watan Oktoba, 2024

0634 GMT — Sabbin hare-haren da Isra'ila ta kai a sassa daban-daban na Gaza sun kashe Falasɗinawa aƙalla 29, ciki har da mata da yara, a cewar jami'an kiwon lafiyar Falasɗinu.

Majiyoyi sun ce dakarun Isra'ila sun kai hari a yankuna da dama da suka haɗa da Khan Younis, sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da na Jabalia.

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 42,000 a yaƙin da take yi a Gaza, a cewar hukumomin kiwon lafiyar yankin, galibinsu mata da yara.

Yaƙin ya lalata yawancin yankin Gaza tare da korar kusan kashi 90 cikin ɗari na mutanen yankin su miliyan 2.3.

2241 GMT —An ɓoye Netanyahu a wani wuri don tsoron hari daga Hezbollah

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar wa Amurka cewa dakarunsa za su kai hari kan cibiyoyin sojojin Iran, ba tashar makamashin nukiliya ko rijiyoyin man fetur ba bayan da Shugaba Joe Biden ya gargaɗe shi game da kai hari kan tashar ta nukiliya, a cewar wasu rahotanni.

Jami'ai biyu da ba sa so a ambace su, ciki har da wani jami'in Amurka, sun ce Netanyahu ya tabbatar da cewa zai kai hari kan cibiyoyin sojin Iran a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Biden a makon jiya, a cewar jaridar The Washington Post.

2113 GMT — An ɓoye Firaministan Isra'ila Netanyahu a wani wuri mai tsaro a asibiti bayan an ji ƙarar jiniya

An garzaya da Firaminista Benjamin Netanyahu wani wuri mai cikakken tsaro a cikin asibiti da ke arewacin Isra'ila bayan an ji ƙarar jiniya da ke nuna yiwuwar kai masa harin roka daga Lebanon ranar Lahadi.

Lokacin da jiniyar ta yi ƙara, Netanyahu yana Asibitin Hillel Yaffe da ke birnin Hadera, inda ya ziyarci sojojin Isra'ila da suka jikkata sakamakon harin jirgi mara matuƙi da ƙungiyar Hezbollah ta kai musu inda ta kashe huɗu daga cikinsu tare da jikkata gommai, a cewar kafar watsa labaran gwamnatin Isra'ila KAN.

Bayan jin ƙarar jiniyar, jami'an tsaron da ke tare da Netanyahu sun ɗauke shi zuwa wani wuri mai cikakken tsaro da ke cikin asibitin, in ji KAN.

Lokacin da jiniyar ta yi ƙara, Netanyahu yana Asibitin Hillel Yaffe da ke birnin Hadera, inda ya ziyarci sojojin Isra'ila da suka jikkata ranar Lahadi sakamakon harin jirgi mara matuƙi da ƙungiyar Hezbollah ta kai musu inda ta kashe huɗu daga cikinsu./Hoto: Reuters
#