Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0600 GMT — Sarkin Jordan ya ce an wurga 'magunguna na bukatun gaggawa' a Gaza
Jiragen sojin saman Jordan sun wuwwurga magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitocin tafi-da-gidanka da ke yankin Gaza da aka mamaye, a cewar Sarki Abdullah II da safiyar Litinin.
"Sojojin samanmu marasa tsoro sun jefa magunguna da ake bukata cikin gaggawa a asibitin wucin-gadi na Jordan da ke Gaza," in ji sarkin a sakon da ya wallafa a shafin X.
0534 GMT — Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta aika da jirgin ruwan nukiliya Gabas ta Tsakiya
Rundunar Sojin Ruwan Amurka ta ce aika da jirgin ruwan nukiliya yankin Gabas ta Tsakiya.
“Ranar 5 ga watan Nuwamba, jirgin ruwa samfurin Ohio-class ya isa yankin da ke karkashi ikon Amurka,” in ji sanarwar da Cibiyar Tsare-Tsare ta Amurka (CENTCOM) ta wallafa a shafin X.
Amurka ta aika da jirage biyu yankin Gabas ta Tsakiya tun daga ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kaddamar da farmakin Operation Al Aqsa Flood a Isra'ila.
0400 GMT — Adadin mutanen da suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 9,770
Ma'aikatar Kiwon Lafiya a Gaza ta ce ya zuwa ranar Lahadi mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Zirin Gaza sun kai 9,770.
“Mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba sun kai 9,770, cikinsu har da kananan yara 4,800 da mata 2,550,” in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
Ta kara da cewa a cikin awa 24 da suka wuce Isra'ila ta kashe Falasdinawa 270.