Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 241 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,550 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 82,959 sun jikkata, a cewar jami'ai.
1144 GMT — Netanyahu ya yi barazanar ɗaukar 'mataki mai ƙarfi' kan Lebanon
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Laraba ya aika da gargaɗi mai tsauri ga ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, inda ya jaddada cewa sojojin Isra’ila sun shirya ɗaukar “mataki mai ƙarfi” kan Lebanon.
Netanyahu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a lokacin wata ziyara da ya kai arewacin Kiryat Shmona da Isra’ila ta mamaye wanda dakarun Hezbollah suka kai wa hare-hare.
“Mun shirya ɗaukar mataki mai ƙarfi a arewaci” kan Lebanon, kamar yadda Netanyahu ya bayyana a shafinsa na X tare da wani bidiyo da ya ɗauka a lokacin da yake rangadi a arewaci kusa da iyakar Lebanon.
1005 GMT — Sojojin Isra'ila tara sun jikkata bayan fashewar wani abu a sansaninsu
Sojojin Isra'ila guda tara sun jikkata sakamakon fashewar wani abu a sansaninsu da ke kudanci, a cewar wata sanarwa da rundunarsu ta fitar
Sanarwar da aka fitar ranar Talata da tsakar dare ta ce an kai dukkan sojojin da suka jikkata asibiti amma biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Ta ƙara da cewa an ƙaddamar da bincike kan fashewar.
Sai dai jaridar The Jerusalem Post ta ruwaito cewa wata gurneti ce ta fashe bayan sojojin sun kammala samun horo.
0211 GMT — Amurka ta ce har yanzu ana dakon martanin Hamas kan yarjejeniyar tsagaita wuta
Ana ci gaba da dakon martanin ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas kan ƙudirin tsagaita wuta na shugaban Amurka Joe Biden, kamar yadda mashawarcin Fadar White House kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya shaida wa manema labarai.
"Muna jiran martani daga Hamas" ta hannun masu shiga tsakani na Qatar, in ji Sullivan.
Sullivan ya ƙara da cewa daraktan CIA Bill Burns zai kasance a Doha don tuntubar masu shiga tsakani na Qatar kan shawarar tsagaita wuta a Gaza. Qatar dai na shiga tsakani kan Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ci gaba da kasancewa cikin rudani kuma yana ganin Biden ya yi ɓangaranci a cikin shawarar da ya bayar, yayin da abokansa masu tsattsauran ra'ayi ke ƙin duk wata yarjejeniya da Hamas. Sun yi barazanar karya gwamnatin hadin gwiwa da Netanyahu idan ya amince da yarjejeniyar Biden.
A halin da ake ciki kuma kakakin Hamas ya nanata cewa ba za su iya amincewa da duk wata yarjejeniya ba, sai dai idan Isra'ila ta bayyana aniyarta "ƙarara" a kan yarjejeniyar tsagaita wuta da ficewa daga Gaza da ta yi wa ƙawanya.
2000 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 19 a Gaza
Likitocin Falasdinawa sun bayyana cewa, hare-haren bama-bamai da na sama da Isra'ila ta kai sun kashe akalla mutum 19 a tsakiya da kudancin Gaza ciki har da 'yan sanda biyu da ke taimakawa wajen kare kai agajin jinƙai a kudancin birnin Rafah.
Mutum 17 daga cikin waɗanda aka kashe ɗin sun rasa rayukansu ne a wasu hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kan sansanonin Bureij da Maghazi da kuma birnin Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza, kuma da sanyin safiyar Larabar nan tankokin Isra'ila sun yi luguden wuta a wani yanki da ke gabashin sansanin Nuseirat, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.
Wasu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters ta wata hanyar manhajar tattaunawa cewa sabon bala'in da sojojin Isra’ila suka jawo na haifar da firgici, inda wasu iyalai da ke zaune a Maghazi suka fara tsere wa luguden wuta da tankokin yaki, inda harsashi hudu suka fado kusa da wani asibiti a sansanin.