Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 179 - ya kashe Falasdinawa akalla 32,916 tare da raunata wasu 75,494 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki.
1453 GMT — Netanyahu ya tabbatar da batun kashe ma'aikatan agaji a Gaza
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da cewa sojojin Isra’ila sun kashe ma’aikatan agaji a Gaza.
A ranar Litinin ne sojojin na Isra’ila suka kai hari kan ma’aikatan agajin World Central Kitchen na Amurka inda suka kashe bakwai.
Netanyahu ya ce “dagangan aka kashe ma’aikatan ba” kuma za a gudanar da bincike,” kamar yadda jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta ruwaito.