Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kwana na 245 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 36,731— kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 83,530 sun jikkata, a cewar jami'ai.

Kai-tsaye: MDD ta yanke shawarar sanya Isra'ila cikin jerin masu cutar da yara

1304 GMT — MDD ta yanke shawarar sanya Isra'ila cikin jerin masu cutar da yara

Majalisar Dinkin Duniya ta yanke shawarar saka Isra'ila cikin jerin sunayen kasashe da kungiyoyin da ke cutar da yara a yankunan da ake rikici.

Shugaban MDD Antonio Guterres ya sanar da mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila a birnin Washington Manjo Janar Hedi Silberman kan matakin, kamar yadda kafar yada labarai ta Isra'ila ta rawaito.

An ba da rahoton cewa Guterres ya bayyana cewa za a saka Isra'ila a cikin jerin masu laifi.

Kafar yada labaran ta rawaito masu sharhi na cewa: "Shigar da Isra'ila a cikin jerin masu aikata laifuka yana da matukar matsala kuma yana iya sa kasashen duniya su ƙaƙaba wa Isra'ila takunkumin sayen makamai.

1051 GMT — Yawan Falasdinawan da suka mutu a yakin Gaza ya kai 36,731 — Ma'aikatar Lafiya

Aƙalla Falasɗinawa 36,731 aka kashe tun lokacin da Isra'ila ta ƙddamar da yaƙi a Gaza a watan Oktoban bara, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta yankin da aka yi wa ƙwanya ta faɗa a wata sanarwa, inda ta ƙara da cewa an kuma jikkata mutum 83,530.

1000 GMT –– Kashi 40 cikin 100 na Jamusawa na goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta –– Bincike

Jamusawa da dama na goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta, kamar yadda wani bincike ya nuna.

Kashi 40 cikin 100 na mutanen da suka ba da amsa a binciken sun ce ya kamata Jamus ta amince da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin mai cin gashin kanta, yayin da kashi 27 suka ce suna adawa da hakan. Kusan kashi 33 kuma sun zama 'yan ko oho.

Jam'iyyar Olaf Scholz, shugaban gwamnati ƙasar ta ƙawancen masu sassaucin ra'ayi ta sha yin biris da kiraye-kirayen da ake yi mata na goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta, tana mai musanta cewa yanayin da ake ciki a yanzu ba zai ba da damar ɗaukar wannan matakin ba.

Wata cibiya ta YouGov ce ta kaɗa ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar a tsakanin mutum 2,295 daga ranar 31 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Yuni.

0925 GMT –– Spain ta ce 'dole ta yi duk abin da ya dace don saka Isra'ila bin umarnin Kotun Duniya

"Dole ne mu yi duk mai yiwuwa don ganin Isra'ila ta yi biyayya ga hukuncin Kotun Duniya (ICJ)," in ji Ministan Harkokin Wajen Spain.

“Abin da muka gani a cikin ‘yan kwanakin nan shi ne matakan taka tsantsan… na wajibi ga kowane bangare… ba a bin su… kasancewar ba sa bambance hare-haren soji da na farar hula, cewa suna kai hari asibitoci da makarantu… ba son yin biyayya ba ne," in ji Jose Manuel Albares a wata hira da jaridar El Pais ta Spain ta buga.

Matakin dai ba wai don "a yi adawa da Isra'ila ba ne" amma don "dakatar da yakin," kamar yadda ya fada wa El Pais, ya kara da cewa Spain ta riga ta fara aiki kan wani rahoto, wanda zai iya wuce shafuka 100, kan lamarin.

“A cikin wannan takarda, muna goyon bayan ayyukan kotun, ba tare da yin riya cewa mu muka maye gurbinta ba,” in ji Ministan.

Da aka tambaye shi ko ya kamata a sanya wa Isra'ila takunkumi idan ba ta bi su ba, Albares bai amsa kai tsaye ba, a maimakon haka ya ce dole ne kasashe su yi duk mai yiwuwa don tilasta wa gwamnatin Isra'ila yin hakan.

#