Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 87 tana yi a Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 21,822 tare da jikkata 56,451 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da ragargazar garuruwa da birane da sansanonn 'yan gudun hijira.
0320 — Mayakan Al-Qassam Brigades sun harba rokoki birnin Tel Aviv da kewayensa
Mayakan Al-Qassam Brigades, wato bangaren soji na kungiyar Falasdinawa ta Hamas, sun harba manyan rokoki daga Zirin Gaza zuwa birnin Tel Aviv na Isra'ila da garuruwan da ke kewayensa da sanyin safiyar Litinin, abin da ya sa jiniya ta yi ta kuka.
Gidan rediyon Rundunar Sojin Isra'ila ya ce haka kuma an harba rokoki a biranen Rishon Lezion, Lod, Ramla, Bnei Brak da Sderot baya ga wani matsugunin Yahudawa mai suna Modi'in Illit da ke tsakiyar Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.
A wani sako da suka wallafa a manhajar Telegram, mayakan Al-Qassam Brigades sun tabbatar da cewa sun harba bama-bamai a Tel Aviv da kewayensa.
"Al-Qassam Brigades na yin luguden wuta da makaman roka samfurin M90 a birnin Tel Aviv da kewayensa domin yin raddi ga kisan kiyashin da Yahudawa suke yi wa fararen-hula,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta nuna bidiyoyin harin rokokin da kungiyar ta kai.
Babu bayani kan ko hare-haren sun yi sanadin mutuwa ko jikkatar wani ko wasu.
0000 GMT —Isra'ila za ta sallami wasu sojojinta na shirin ko-ta-kwana daga yakin Gaza
Rundunar sojin Isra'ila za ta sallami wasu daga cikin sojojinta na shirin ko-ta-kwana da ke yaki a Gaza, a wani mataki da ta ce zai taimaka wa tattalin arzikinta a yayin da kasar take shirin kaddamar da dogon yaki a yankin.
"Wasu daga sojojin shirin ko-ta-kwana za su koma wurin iyalansu da kuma bakin aikinsu a wannan makon," a cewar kakakin rundunar sojin Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari.
"Hakan zai bunkasa tattalin arziki, sannan ya ba su damar samun kuzari a jikinsu gabanin ayyukan da za su yi a wannan shekarar, kuma za mu ci gaba da yaki, kana za mu bukace su."