Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 30 a yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,271, ko da yake sabbin alƙaluma sun nuna cewa waɗanda ta kashe sun zarta 62,000.
Litinin, 17 ga Fabarairu, 2025
0604 GMT –– Majalisar tsaron Isra'ila na shirin tattaunawa kan zagaye na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, bayan Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun amince da matsaya iri ɗaya da ke sukar Hamas da Iran.
Rubio ya je Isra'ila ne a matakin farko na ziyararsa a Gabas ta Tsakiya a matsayinsa na babban jami'in diflomasiyya na gwamnatin Shugaba Donald Trump, kuma zai tafi Saudiyya a ranar Litinin.
"Ba zai yiwu Hamas ta ci gaba da kasancewa fannin soji ko kuma dakarun gwamnati ba... dole a kawar da ita," in ji Rubio da yake magana a game da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa wadda ta kwashe fiye da wata 15 tana gumurzu da Isra'ila a yankin Gaza kafin a amince da tsagaita wuta ranar 19 ga Janairu.
2257 GMT — Kashi 30 ne kacal na motocin kayan agaji ya isa Gaza a kwana biyu da suka wuce
Adadin manyan motocin da ke ɗauke da kayan agaji da suka shiga a kwanaki biyu da suka gabata bai wuce kashi 30 cikin ɗari ba, a cewar ofishin watsa labarai na Gaza, wanda ya ce hakan ya faru ne sakamakon katsalandan ɗin da dakarun Isra'ila suke yi a yunƙurin ganin an kai kayan agaji yankin.
Kawo yanzu manyan motocin kayan agaji guda 180 ne suka shiga Gaza, adadin da ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da motoci 600 da aka amince su shiga yankin a yarjejeniyar tsagaita wutar da aka ƙulla tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa da ofishin watsa labarai na Gaza ya fitar
Ƙarin labarai????
2103 GMT — Rubio ya ce kasancewar ƙarin 'Isra'ilawa' a Gabas ta Tsakiya zai sa duniya ta ƙara 'zama lafiya'
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi iƙari ranar Lahadi cewa duniya za ta fi samun zaman lafiya idan aka samun ƙarin Isra'ilawa da ke zaune a yankin Gabas ta Tsakiya.
"Idan aka samu ƙarin Isra'ila a Gabas ta Tsakiya, duniya za ta fi zama lafiya da aminci," in ji Rubio a wani tarin manema labarai da ya gudanar da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Yammacin Birnin Ƙudus, a cewar wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Isra'ila ya fitar.
Kazalika ya jaddada aniyar mahukuntan Washington ta goyon bayan Isra'ila.