Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Lokacin surutu ya kare, ya kamata a dauki mataki kan rikicin Gaza - Shugaban Iran Raisi

0750 — Lokacin surutu ya kare, ya kamata a dauki mataki kan rikicin Gaza - Raisi

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ranar Asabar ya ce lokacin surutu ya kare don haka yanzu lokacin daukar mataki ne a kan rikicin Gaza a yayin da yake kan hanyar tafiya Sudiyya domin halartar taron Kasashen Larabawa da na Musulmai.

"Batun Gaza ba na yin surutu ba. Ya kamata a dauki mataki," in ji Raisi a filin jirgin saman Tehran kafi ya tashi zuwa birnin Riyadh na Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Ya kara da cewa: "A yau, hadin kan kasashen Musulmai yana da matukar muhimmanci."

Shugaba Ebrahim Raisi ya ce hadin kan kasashen Musulmai yana da matukar muhimmanci./Hoto:Reuters

0700 — Isra'ila tana harba bama-bamai da kashe 'jarirai da mata da tsofaffi' a Gaza — Shugaban Faransa Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga Isra'ila ta daina harba bama-bamai kan fararen-hula a Gaza, yana mai cewa babu wata hujja ta yin haka.

A hira da BBC, Macron ya ce Isra'ila tana da ikon kare kanta bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, sai dai ya kara da cewa: "Ana harba bama-bamai da kashe wadannan jarirai da mata da tsofaffi. Babu wata hujja ta yin haka. Saboda haka muna kira ga Isra'ila ta daina."

Tsarin kiwon lafiya na Gaza "ya durkushe" amma duk da haka ana tura magunguna na musamman," a cewar jami'in WHO. / Hoto: AA

0629 GMT — An zargi Isra'ila da 'kaddamar da yaki' a asibitocin Gaza masu cike da jama'a

Ana ci gaba da gumurzu a kusa da asibotocin Gaza masu cike da jama'a, inda jami'an Falasdinu suka ce Isra'ila tana jefa musu abubuwan fashewa da yin luguden wuta.

"Yanzu haka Isra'ila ta kaddamar da yaki a asibitocin Gaza," a cewar Mohammad Abu Selmeyah, daraktan Asibitin Al Shifa.

Daga bisani ya ce Isra'ila ta kashe mutum akalla 25 a makarantar Al-Buraq da ke Birnin Gaza, inda mutanen da ta rusa wa gidaje suke samun mafaka.

Jami'ai a Gaza sun ce Isra'ila ta harba rokoki a harabar Asibitin Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a yankin, da safiyar Juma'a, sannan ta lalata Asibitin Indonesia kuma an cinna wuta a cibiyar kula da masu ciwon kansa ta Asibitin Nasser Rantissi.

#