Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki

0850 GMT — Kungiyar Hezbollah ta ce ta kakkabo jirgin Isra'ila maras matuki

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta ce ta kakkabo jirgin Isra’ila maras matuki da makami mai linzami a yankin Galilee Panhandle.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar da safe inda ta ce ta harba makamin nata da misalin karfe 1:45 agogon kasar, (23:45 agogon GMT).

Ta bayyana cewa ta hango a lokacin da tarwatsatsun sassan jirgin ke faduwa ta yankin na Galilee Panhandle.

Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da sanarwa domin gasgatawa ko kuma karyata ikirarin na Hezbollah ba.

Sama da Falasdinawa 12,000 Isra’ila ta kashe zuwa yanzu, inda sama da 8,300 yara ne da mata, haka kuma ta raunata sama da 30,000.

#