Hare-haren da Isra'ila ta kwashe 67 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,205, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 49,645 sun jikkata kana dubban na binne a karkashin baraguzan gine-gine

KAI-TSAYE: Jirgin Isra'ila maras matuki ya kashe karin Falasdinawa hudu

0755 GMT — Jirgin Isra'ila maras matuki ya kashe karin Falasdinawa hudu

Isra’ila ta kashe Falasdinawa hudu a wani hari ta sama da ta kai a birnin Jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye da kuma sansaninta na ‘yan gudun hijira.

Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza tare da Kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ne suka tabbatar da hakan.

Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito cewa akwai karin mutum guda da aka raunata a unguwar al Sibat da ke birnin Jenin.

Daraktan asibitin Jenin ya shaida cewa an kai harin ne kai tsaye kan Falasdinawa. Haka kuma kamfanin dillancin labaran ya tabbatar da cewa sojojin na Isra’ila sun yi wa asibitoci uku kawanya a yankin.

0149 GMT — An kai wa jirgin ruwa hari a Bahar Maliya yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Gaza

Wasu cibiyoyin leken asiri masu zaman kansu sun ce an kai wa wani jirgin ruwa hari a gabar tekun Yemen na Bahar Maliya.

Harin da aka kai kan jirgin ruwan ya zo ne a daidai lokacin da 'yan tawayen Houthi na Yemen ke ci gaba da yin barazana a kan safarar jiragen ruwa na kasuwanci a yankin saboda yaƙin da Isra'ila ke yi a zirin Gaza.

'Yan Houthi dai ba su dauki alhakin kai harin ba, ko da yake kakakin rundunar 'yan tawayen Birgediya Janar Yahya Saree ya ce wata muhimmiyar sanarwa za ta fito daga gare su nan da sa'o'i masu zuwa.

Cibiyoyin leken asiri masu zaman kansu Ambrey da Dryad Global sun tabbatar da cewa harin ya afku ne a kusa da mashigin Bab al-Mandeb da ke raba gabashin Afirka da yankin Larabawa, amma sun ce ba su da wani karin bayani.

Wani makami mai linzami da aka harba daga yankin kasar Yemen da ke karkashin ikon Houthi ya kai hari kan wani jirgin ruwan dakon kaya na kasuwanci, inda ya yi sanadin tashin wuta da jawo ɓarna, kamar yadda jami'an tsaron Amurka biyu suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani jami'in ya ce harin da aka kai kan jirgin ruwan na STRINDA ya faru ne daga tazarar kilomita 60 a arewacin gabar tekun Bab al Mandab.

Jami'an sun ce jirgin ruwan Amurka na agaji na Mason ya je wurin kuma yana bayar da agaji. Ba a dai fayyace ko STRINDA na da wata alaka da Isra'ila ko kuma yana kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa ta Isra'ila ba ne.

0134 GMT — A shirye Isra'ila take don sabuwar yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas: Kafafen yada labarai na cikin gida

Isra'ila a shirye take ta dawo da tuntubar masu shiga tsakani domin ganin an sako wasu 'yan Isra'ila da ake tsare da su a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka rawaito.

Sabuwar yarjejeniyar musayar za a gudanar da ita ne a cikin tsarin sulhu na jinƙai kuma ya haɗa da mata da ke cikin zaman talala da marasa lafiya da waɗanda suka jikkata da kuma tsofaffi, in ji tashar Channel 12 ta Isra'ila.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce har yanzu ƙungiyar Hamas na riƙe da fursunoni 137 da suka haɗa da 'yan Isra'ila 126 da 'yan ƙasashen waje 11.

Tashar talabijin ta Channel 12 ta ce jami'an Isra'ila sun yi imanin cewa, ba zai yiwu a cim ma sabuwar yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas a mako mai zuwa ba, amma har yanzu Isra'ila ta yi imanin bude wata sabuwar hanya, ta hancyar cin gajiyar matsin lambar da Hamas ke fuskanta sakamakon yaƙin da ake yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Tashar ta rawaito majiyar soji tana cewa tsananin fadan ya fara bude hanyar yin musanyar juna da ba za a rasa ba.

18:07 GMT –– Ɓarnar da aka yi a Gaza ta fi muni fiye da ta Yakin Duniya na II na Jamus — Borrell

Babban jami'in diflomasiyyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce halin da ake ciki a Gaza "mummunan bala'i ne, mai ban tsoro", inda ɓarnar da aka samu ta fi wacce aka yi wa Jamsu muni a yaƙin duniya na biyu.

Martanin da sojojin Isra'ila suka yi kan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba ya haifar da "yawan asarar rayukan fararen hula", in ji Borrell a jawabin da ya yi a taron ministocin harkokin wajen EU.

Ya ce EU ta kuma firgita da tashe-tashen hankula a Yammacin Kogin Jordan da masu tsattsauran ra'ayi ke yi, ya kuma yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Isra'ila ta dauka na amincewa da ƙarin wasu gidaje 1,700 a Birnin Kudus, lamarin da Brussels ke ganin ya saba wa dokokin kasa da kasa.

#