Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 282 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 38,584 — galibinsu mata da yar –– sannan ya jikkata mutum sama da 88,881, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ɓaraguzai.
1351 GMT — Jami’an kare farar hula a Gaza sun zaƙulo gawawwaki 21 na Falasɗinawa daga cikin ɓarguzai a ranar Lahadi bayan wani hari da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.
Wata majiya daga bangaren kiwon lafiya ta bayyana cewa an gano gawar mutum shida sakamakon harin da Isra’ila ta kai a birnin Rafah inda aka kai su asibitin Khan Younis.
Haka kuma an ƙara zaƙulo wasu gawawwakin uku daga cikin ɓaraguzai a yammacin Gaza, kamar yadda Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta bayyana a wata sanarwa.
Jami’an sun ƙara gano wasu gawawwakin goma a unguwar Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin Gaza. Sai kuma mazauna sansanin gudun hijira na Nuseirat sun gano gawawwakin mutum biyu a tsakiyar Zirin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.