Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 300, kuma ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 39,445, galibinsu mata da yara tare da raunata wasu 91,073. Sannan ana kiyasin wasu sama da 10,000 na binne a karkashin baraguzan gidajen da aka rusa.

Kai-tsaye: Jagoran addini na Iran Khamenei ne zai jagoranci jana'izar Ismail Haniye na Hamas

0056 GMT — Jagoran addini na Iran Khamenei ne zai jagoranci jana'izar Ismail Haniye na Hamas

Tashar talabijin ta ƙasar Iran Presstv ta ce Jagoran addinin Musulunci na kasar Ali Khamenei zai jagoranci sallar jana'izar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, kana kuma jagoran tattaunawar zaman lafiya Ismail Haniyeh.

Tashar talabijin ta Press TV ta ƙara da cewa, za a gudanar da jana'izar ne a Tehran babban birnin kasar Iran.

Da sanyin safiyar Laraba ne Isra’ila ta kashe Haniyeh a birnin Tehran, harin da ya janyo barazanar daukar fansa kan Isra’ila tare da ƙara nuna fargabar cewa yaƙin kisan kare dangi na Tel Aviv a Gaza yana rikidewa zuwa yaɗuwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

2211 GMT — Kwamitin Tsaro na MDD ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas

Wakilan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da kisan gillar da Isra'ila aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin kasar Iran, yayin da wakilan dindindin na Amurka da Birtaniya suka zargi Iran da tada zaune tsaye a yankin.

Kwamitin ya kira wani zama na gaggawa kan kisan Haniyeh bisa bukatar Iran, wadda ke samun goyon bayan Rasha da Aljeriya da China.

Da yake jawabi a wajen taron, jakadan kasar China Fu Cong ya ce, kasarsa ta yi kakkausar suka ga kisan gillar da aka yi wa Haniyeh.

Yayin da ya kira lamarin "yunkuri na neman kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya," Cong ya jaddada cewa, "China ta damu matuka game da kara ta'azzara tarzoma a yankin da wannan lamari zai iya haifar da shi."

Hakazalika wakilin Aljeriya a Majalisar Dinkin Duniya Amar Bendjama ya ce: "Muna kan hanyar ganin bala'i," ya kara da cewa harin na Isra'ila "aikin ta'addanci ne" wanda ya saɓa wa dokokin kasa da kasa da kuma ikon Iran.

"Wannan ba wai hari ne kawai kan mutum daya ba, wani mummunan hari ne kan tushen dangantakar diflomasiyya, da tsarkin mulkin kasa da kuma ka'idojin da ke tafiyar da tsarinmu na duniya," in ji shi.

#