Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
2300 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 51, ta jikkata gommai a sansanin 'yan gudun hijira na Gaza — Faladinu
Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 51 sannan ta jikkata gommai a harin da ta kai ta sama a sansanin 'yan gudun hijira na Al Maghazi da ke tsakiyar Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA.
Kakakin Ma'aikatar Lafiya ta Gaza, Ashraf al-Qidra, ya ce an kashe mutane da dama ba tare da ya bayar da hakikanin alkaluman wadanda suka mutu ba, sai dai ya kara da cewa gommai sun jikkata kuma suna kwance a dandarin kasa a sashen bayar da agajin gaggawa na asibiti.
Maghazi yana yankin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.
Ganau sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hare-haren sun fada kan gidaje da dama.
"Isra'ila ta kai hari ta sama a gidajen makwabtana da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al-Maghazi, an lalata tagogin gidan da ke kusa da nawa," in ji Mohammed Alaloul, mai shekara 37, wani dan jarida da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Anadolu na Turkiyya.
Alaloul ya shaida wa AFP cewa harin ya yi sanadin mutuwar 'ya'yansa Ahmed, dan shekara 13 da kuma Qais, dan shekara hudu, tare da dan uwansa. An jikkata mahaifiyarsa da matarsa da kuma wasu 'ya'yansa biyu.