Yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da yankin Gaza ta shiga kwana na 16 — bayan dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa fiye da  47,498. Kazalika Netanyahu ya tafi Amurka domin tattaunawa da Trump.

Kai-tsaye: Isra'ila tana yin luguden wuta a sansanin Jenin kamar yadda ta yi a Gaza — Falasɗinu

Litinin, 3 ga watan Fabrairu, 2025

2133 GMT — Isra'ila tana yin luguden wuta a gidajen jama'a da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jenin kamar yadda ta yi a yankin Gaza da ta mamaye, in ji wani jami'in Falasɗinu a hira da kamfanin labarai na Anadolu Agency.

Kamal Abu al Rub, gwamnan Jenin da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, ya ce hukumomin Isra'ila suna aiki tuƙuru domin ruguza sansanin ta yadda ba za a iya zama a gidaje da sauran matsugunan da ke cikinsa ba.

"Sojojin Isra'ila sun karkata zuwa Gaɓar Yammacin Kogin Jordan daga Zirin Gaza a yaƙin da suke yi, kuma abin da ke faruwa a sansanin Jenin ya yi kama da kisan ƙare-dangin da Isra'ila ta yi a Gaza," in ji shi.

Abu al Rub ya ƙara da cewa hare-haren bama-baman da Isra'ila take yi a sansanin si ne irinsa "na farko tun shekarar 2002, bayan yaƙin da ya lalata sansanin a wancan lokacin."

#