Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 309, inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 39,699 — mafi yawansu mata da yara — ya kuma raunata sama da mutum 91,722. Ana ƙiyasin fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa.

Kai-tsaye: Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a makaranta a Gaza, ta kashe fiye da Falasɗinawa 100

0230 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 ta kuma jikkata da dama a wani hari da ta kai wata makaranta a Birnin Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labaran gwamnati na WAFA ya bayyana.

Kamfanin dillancin labaran na Falasinawa WAFA ya ce tankokin yaƙin Isra'ila sun yi lugude kan makarantar, wacce ta zama mafaka ga Falasɗinawan da suka rasa gidajensu.

"An yi wa fiye da mutum 40 shahada an jikkata da dama bayan harin na Isra'ila a makarantar Al-Tabai'een a yankin Al-Sahaba a Birnin Gaza," kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan yankin Mahmoud Basal ya wallafa tun da farko a saƙon da ya wallafa a Telegram.

0052 GMT — An kai wa sojojin Amurka hari a Syria

An kai wa sojojin Amurka hari da jirage marasa matuƙa a Syria, kamar yadda wani jami'in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, duk da dai babu wanda ya ji rauni kamar yadda rahotannin farko-farko suka nuna.

"Rahotannin farko ba su nuna cewa an samu wanda ya ji rauni ba, sai dai jami'an lafiya na ci gaba da duba abubuwan da suka faru a wajen. A yanzu haka muna nazari kan ɓarnar da aka yi," kamar yadda jami'in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana.

Amurka tana da sojoji da dama a Gabas ta Tsakiya, da adadinsu ya kai kimanin 45,000, da sansanoni da dama, da jiragen yaƙi na sama da na ruwa da yawa, abin da ya sa ake nuna damuwa kan yiwuwar ɓarkewar yaƙi a yankin.

A yanzu haka Amurka na da dakaru na musamman da sojoji kimanin 900 a Syria don taimaka wa ƙungiyar ta'addanci ta YPG/PKK, wacce take amfani da sunan SDF.

Amurka na da na ƙananan sansanoni kamar wajen haƙar mai na al-Omar da Al-Shaddadi, mafi yawa a arewa maso gabashin ƙasar, da kuma wani ƙaramin sansanin tsaro na soji, da aka fi sani da sansanin Al-Tanf kusa da iyakar Syria da Iraƙi da Jordan.

#