Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 384, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,792 da jikkata fiye da 100,000, kan ana ƙiyasi mutum fiye da 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,574 a hare-hare a Lebanon.
Alhamis, 24 ga watan Oktoba, 2024
2341 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari ta sama fiye da 17 a yankunan da ke wajen kudancin Beirut babban birnin Lebanon, a wani matai da ake gani a matsayin ɗaya daga cikin manyan hare-hare da ta ka a birnin.
Kamfanin dillancin labarai na Lebanon, National News Agency (NNA), ya ruwaito cewa Isra'ila ta kai hare-hare huɗu ta sama a yankin Laylaki, waɗanda suka rusa rukunin gidaje shida tare da haddasa gobara da ta watsu zuwa sauran sassan yankin.
Ya ƙara da cewa jirin yaƙin Isra'ila ya rusa ofishin gidan talbijin na Al Mayadeen TV wanda ake alaƙantawa da ƙungiyar Hezbollah, wanda ke cikin rukunin wasu gine-gine.
Ƙarin labarai ????
0151 GMT — Isra'ila ta kai hari kan wasu gidajen jama'a a Damascus
Kafar watsa labarai t gwamnatin Syria ta ce Isra'ila ta kai hari a wani gini da jama'a ke zama a birnn Damascus.
"Rahotannin da aka fara samu sun nuna cewa Isra'ila ta kai hari a wani gini da jama'a ke zama a yankin Kafr Sousa na birnin Damascus," a cewar kamfanin dillancin labarai na Sana, ko da yake bai yi ƙarin bayani ba.