Hare-haren da Isra'ila ta kwashe 70 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,787, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 50,897 sun jikkata kana dubban na binne a karkashin baraguzan gine-gine

KAI-TSAYE: Isra'ila ta watsa takardun ingiza 'yan Gaza yin leken asiri kan shugabannin Hamas da alkawarin tukwici

0139 GMT — Isra'ila ta watsa takardun ingiza ƴan Gaza yin leken asiri kan shugabannin Hamas da alkawarin tukwici

Sojojin Isra'ila sun jefar da wasu takardu a fadin Gaza da aka yi wa ƙawanya, inda suke zuga Falasdinawa da suka rasa matsugunansu yin leƙen asiri ga shugabanninsu tare da bayar da tukwicin kudi ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kame wasu jiga-jigan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.

Masu fafutuka na Falasdinu sun yi ta yada hotunan takardun a intanet, inda sojojin suke tunzura mazauna yankin don bayar da bayanai game da Yahya Sinwar, shugaban Hamas a Gaza da kuma ɗan'uwansa Muhammed Sinwar, fitaccen shugaban soji a rundunar Hamas ta Al Qassam Brigades da Mohammed Deif, babban kwamandan Al Qassam Brigades, da Rafaa Salameh, wanda ke ba da umarni ga bataliyar dakarun da ke Khan Younis.

Takardun da ke dauke da suna da kuma tambarin sojojin Isra'ila, sun ce: "Al'ummar Gaza, Hamas ta rasa ƙarfinta, kuma ƙarshen Hamas ya kusa."

"Don makomarku, ku ba da bayanan da za su ba mu damar kama waɗanda suka jawo lalacewar Zirin Tekun."

"Wadanda suka bayar da bayanai za su samu ladan kudi kamar haka: Bayani kan

  • Yahya Sinwar, dala 400,000
  • Muhammed Sinwar, dala 300,000
  • Rafaa Salameh, dala 200,000
  • Mohammed Deif, dala 100,000."

Sojojin sun hada da bayanan tuntuɓar juna da sunan wani asusun Telegram a cikin takardun.

0130 GMT — An yi asarar rayuka yayin da tankokin yaki da jiragen Isra'ila suka yi ruwan bama-bamai a Gaza

Tankunan yaƙi da jiragen saman Isra'ila sun tsananta ruwan bama-bamai a yankunan arewacin Gaza na Shejaia da Zeitoun da Daraj da Khan Younis da ke kudancin yankin, in ji mazauna yankin.

Jami'an kiwon lafiya na Falasdinu sun sanar da cewa, an kashe Falasdinawa hudu da suka hada da ƙananan yara biyu, yayin da wasu da dama suka jikkata, a wani harin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai kan wani gida a Khan Younis da ke kudancin Gaza da sanyin safiyar Juma'a.

Isra'ila dai na ci gaba da luguden wuta a tsawon kilomita 40 na Zirin Gaza ba tare da wata alamar dakatar da kai hare-hare ba ko kuma tsagaita wuta da za ta ba da damar isar da kayayyakin more rayuwa da ake buƙata ga fararen hula, domin tsira da rayukansu yayin da aka lalata gidajensu ba.

Sojojin Isra'ila sun yi ƙawanya a gabar tekun zirin tare da lalata da yawa daga cikinsa, inda aka tabbatar da mutuwar kusan mutum 19,000, a cewar jami'an kiwon lafiyar Falasdinu, kuma ana fargabar wasu dubban suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.

2330 GMT — MDD ta bukaci Isra'ila da ta ba da damar shiga Gaza saboda dumbin mutane na fuskantar yunwa

Wani babban jami'in hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP, ya bukaci Isra'ila da ta kara ba da damar shiga Gaza tare da tabbatar da tsaro domin isar da kayan agajin da ake bukata.

Jami'in ya yi nuni da wani bincike da aka yi a tsawon kwanaki bakwai da aka dakatar a yakin da ya nuna cewa rabin al'ummar yankin na fama da yunwa.

Carl Skau, mataimakin daraktan hukumar samar da abinci ta duniya, ya shaida wa taron manema labarai na MDD cewa, ya kamata kuma manyan motocin kasuwanci su fara komawa Gaza saboda yadda manyan kantuna da wasu shaguna suka kasance babu kowa.

Hakan zai bai wa WFP damar sake dawo da tsarin ba da takardun kudi kafin yaƙin wanda ya bai wa Falasdinawa a Gaza damar sayen abinci da sauran muhimman abubuwa, in ji shi.

Skau, wanda ya ziyarci Gaza a karshen mako, ya ce lamarin na ƙara taɓarɓarewa da hargitsi, inda MDD ta kasa kai kayan abinci zuwa tsakiyar ko arewacin Gaza da Isra'ila ke kai farmakin soji.

“Abin takaicin kuma shi ne tara daga cikin mutane 10 ba sa cin abinci sosai ko kuma ba sa cin abinci a kowace rana, kuma ba su san inda za su samun abinci na gaba ba,” in ji shi.

Mutane suna cikin matsananciyar damuwa da takaici da fushi, kuma sukan yi ƙoƙarin yin rububi a kan kayan agaji da ake saukewa a Rafah da ke kudu, "kuma wannan yana ƙara zama matsala - cewa akwai rashin bin doka da oda," in ji Skau.

Ya kuma kara da gargadin babban jami’in jinƙai na MDD Martin Griffiths cewa ayyukan jinƙai a Gaza na gab da durƙushewa.

#