Wannan shafi yana kawo muku bayanai kan musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas bayan hare-haren da Isra'ila ta kwashe kusan kwana 50 tana kaiwa a Gaza, wadanda suka yi ajalin Falasdinawa 14,854, ciki har da yara 6,150 da mata fiye da 4,000.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta saki kananan yara Falasdinawa 30 da mata uku a yarjejeniyar musaya da Hamas

0400 GMT — Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan laifukan da aka aikata a Isra'ila da Falasdinu

Wasu gungun kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan laifukan da aka aikata a Isra'ila da Falasdinu a wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a ranar Litinin.

Da suke kira ga Isra'ila da hukumar Falasdinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan da hukumomin Gaza da su ba da cikakken hadin kai don yin binciken, sun ce "dole ne a bai wa masu bincike masu zaman kansu abubuwan da suka dace da goyon baya da samun damar da ake bukata don gudanar da bincike cikin gaggawa, da kuma nuna rashin son kai kan laifukan da ake zargin aikatawa a dukkan bangarorin da ke rikici.

"Aikin binciken laifuffukan yaki da cin zarafin bil adama, da suka hada da duk wani aiki na takaitawa ko kisan gilla da azabtarwa ko wasu cin zarafi kan mutuncin dan'adam, wani muhimmin al'amari ne na shari'a," in ji su.

Sun kuma yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki domin ganin an gaggauta hukunta duk wadanda ke da hannu wajen aikata laifukan yaƙi da cin zarafin Bil'adama da kuma sauran laifukan da suka shafi kasa da kasa a rikicin, musamman wadanda ke da alhakin gudanar da ayyukansu.

0330 GMT — Shugaban Hamas a Gaza ya gana da wasu Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su: Kafofin yada labaran Isra'ila

Shugaban kungiyar Hamas ta Falasdinawa a Gaza, Yahya Sinwar, ya gana da wasu mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su a cikin ramukan ƙarƙashin ƙasa a Zirin Gaza, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka rawaito.

Akalla daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ya ce Sinwar ya yi magana da su cikin harshen Ibrananci, kamar yadda jaridar Haaretz ta ruwaito.

Ya ce musu suna cikin aminci tare da Hamas kuma ka da su ji tsoro. Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, hukumar tsaron Isra'ila ta tabbatar da labarin.

2317 GMT — Isra'ila ta saki kananan yara Falasdinawa 30 da mata uku a yarjejeniyar musanya da Hamas

Isra'ila ta saki ƙananan yara Falasdinawa 30 da mata uku "a cikin dare" karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da ta mayar da fursunonin yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya.

Sakin dai ya kawo adadin mata da yara ƙanana Falasdinawa da Isra'ila ta sako a cikin kwanaki hudu na farko na dakatar da yaƙin zuwa 150.

Wadanda aka sako da sanyin safiyar Talata sun hada da Bafalasdiniya mafi ƙarancin shekaru a cikin mutanen, Nofuz Hammad ‘yar shekara 16 da haihuwa, daga unguwar Sheikh Jarrah da ke gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye, wacce tun farko hukumomin Isra’ila suka daure ta shekaru 12 a gidan yari, kuma a yanzu ta sake ta a yarjejeniyar musanya ta Hamas da Isra’ila, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Anadolu ya ruwaito.

2313 GMT — Netanyahu ya amince da sanya Falasdinawa mata 50 cikin jerin sunayen waɗanda za a saki

Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya amince da saka wasu Falasdinawa mata 50 a cikin jerin sunayen da za a sake su idan har an sako wasu 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su daga Gaza.

Sanarwar ta zo ne bayan da masu shiga tsakani na Qatar suka ce tsagaita wuta ta kwana hudu ta amince da ba da damar musayar fursunonin da Isra'ila ke tsare da su, da Falasdinawan da ke cikin gidajen yarin na Isra'ila wanda ya kamata ya ƙare bayan da aka tsawaita wa'adin kwanaki biyu a ranar Litinin.

#