Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta rusa masallatai 56 a Gaza

Isra'ila ta lalata masallatai 192, cikin har da 56 da ta lalata baki daya tun da ta soma kai gari a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gaza a sanarwar da ya fitar Litinin da maraice.

"Hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaza sun lalata masallatai 192, ciki har da 56 da ta rusa baki daya, baya ga coci uku da ta rusa,” a cewar mai magana da yawun ofishin na Watsa Labarai Salama Marouf a taron manema labarai da ya gudanar a Birnin Gaza.

Ya kara da cewa hare-haren sun rusa cibiyoyin kiwo lafiya 192 da kuma motocin daukar marasa lafiya 32 kana sun lalata cibiyoyin kiwon lafiya 113, yayin da asibitoci 16 da cibiyoyin samar da lafiya 32 suka daina aiki.

#