Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 73 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,800, da jikkata wasu fiye da 51,000, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari.
0732 GMT — Isra'ila ta kashe 'yan gudun hijira 90 a wani sansani da ke Gaza
Isra’ila ta kaddamar da munanan hare-hare a Gaza, inda ta kai hari a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewacin birnin, da kuma asibiti a kudanci inda sojojin suka kashe wata matashiya wadda ta rasa kafarta a wani hari na baya da suka kai, kamar yadda hukumomin Falasdinu suka shaida.
Harin da Isra’ila ta kai sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 90, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta Gaza ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Wani makami mai linzami da aka harba a gidan iyalan Shehab ya yi sanadin mutuwar mutum 24, kamar yadda gidan rediyon Aqsa na Hamas ya sanar.
0000 GMT — WHO ta yi tur da 'lalata' asibitin Kamal Adwan na Gaza
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi Allah wadai da "mummunar ɓarnar" da aka yi a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, inda ya kara da cewa akalla majiyyata takwas ne suka mutu.
Daga cikin majinyatan da suka rasu har da wani yaro dan shekara tara, in ji Tedros Adhanom Ghebreyesus a wani sako da ya wallafa a shafin X.
Bayanin nasa ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila suka fice daga asibitin bayan wani samame da suka shafe kwanaki suna yi, suna masu cewa kungiyar Hamas ta yi amfani da shi a matsayin cibiyar bayar da umarni.
Hamas dai ta sha musanta irin wannan ikirarin.
Tedros ya rubuta "@WHO ta yi matukar mamakin yadda aka lalata asibitin Kamal Adwan da ke arewacin #Gaza a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, lamarin da ya sa ba ya aiki kuma hakan ya jawo sanadin mutuwar aƙalla mutum takwas."
Ya kara da cewa, "An ce an tsare ma'aikatan lafiya da dama, kuma WHO da abokan huldarsu na neman bayanai cikin gaggawa kan halin da suke ciki."
0130 GMT — Hukumomin Falasdinu sun bukaci Faransa da ta taimaka wajen warware rikicin 'yan kama wuri zauna a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Hukumomin Falasdinu sun bukaci Faransa da ta taimaka wajen warware hare-haren da 'yan kama wuri zauna ke kai wa Falasdinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan.
A yayin ganawar da Firaministan Falasdinu Muhammad Shtayyeh da takwararsa ta Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna suka yi a birnin Ramallah da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan, Shtayyeh ya jaddada wajabcin matsa wa Isra'ila lamba kan ta daina cin zarafin Falasdinawa a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, ciki har da Gabashin Birnin Ƙudus.
Shtayyeh ya kuma yi kira da a bude dukkan mashigan Zirin Gaza domin ba da damar shigar da kayan agaji da magunguna da man fetur da kuma dawo da ayyukan wutar lantarki da na ruwa.
Har ila yau, ya jaddada muhimmancin goyon bayan Faransa don amincewa da kasar Falasdinu tare da zama cikakiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya.
0020 GMT - Ana yi wa Isra'ila sabbin kiraye-kirayen tsagaita wuta bayan da kisan mutanen da aka yi garkuwa da su ya haifar da fargaba kan ayyukanta a Gaza
Gwamnatin Isra'ila ta fuskanci kiraye-kirayen cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta daga wasu makusantanta na Turai, bayan wasu jerin harbe-harbe da suka hada da kisan da aka yi wa wasu Isra'ilawa uku da aka yi garkuwa da su cikin "kuskure", lamarin da ya kara tayar da hankalin duniya game da yakin da aka kwashe makonni 10 ana yi a Gaza.
Masu zanga-zangar a Isra'ila suna kira ga gwamnatinsu da ta sabunta tattaunawa da gwamnatin Hamas ta Gaza, wadda Isra'ila ta sha alwashin rusawa.
Ana kuma sa ran Isra'ila za ta fuskanci matsin lamba don rage manyan ayyukan yaki a lokacin da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin zai kai ziyara a yau Litinin