Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 408 — ya kashe aƙalla Falasɗinawa 43,799 da jikkata 103,601, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,440 tun Oktoban bara.
1125 GMT –– Akalla Falasdinawa 96 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka jikkata sakamakon hare-haren da jiragen yakin Isra'ila suka kai arewaci da tsakiyar Zirin Gaza a ranar Lahadi, a cewar hukumomin yankin.
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ce jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan wasu gine-gine da gidaje a arewacin birnin Beit Lahia da kuma sansanonin 'yan gudun hijira na Nuseirat da Bureij a tsakiyar Gaza.
Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce sama da mutane 72 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai a Beit Lahia, yayin da wasu Falasdinawa 24 suka mutu, wasu 60 kuma suka jikkata a tsakiyar Gaza.