Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 399 — ya kashe akalla Falasdinawa 43,552 da jikkata 102,765, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,136 tun Oktoban bara.
0544 GMT — Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce mutum 30 da suka hada da kananan yara 13 ne suka mutu a wasu hare-hare biyu da Isra'ila ta kai kan wasu gidaje biyu a arewacin Falasɗinu.
Harin na farko wanda aka kai shi da safiyar Lahadi ya faɗa ne a wani gida da ke Jabalia da ke arewacin Gaza, inda ya kashe aƙalla mutum 25 daga ciki har da yara 13 tare da jikkata sama da mutum 30, in ji hukumar kare farar hular.
Wani harin kuma ya faɗa ne a unguwar Sabra da ke birnin Gaza inda mutum biyar suka rasu, wasu da dama kuma sun ɓata bayan harin.
Hukumar ta kara da cewa, har yanzu akwai fararen hula da dama a karkashin baraguzan ginin.