Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe manomi a sansanin 'yan gudun hijira

1150 GMT — Isra'ila ta kashe kwamandojin Hamas hudu

Dakarun sojin Hamas na Falasdinu sun sanar da kashe kwamandojinsu hudu a Gaza, daga ciki har da Ahmad Ghandour wanda shi ne kwamandan Arewacin Gaza.

“Al Ghandour (Abu Anas) mamba ne a majalisar soji kuma kwamanda ne a Arewaci,” kamar yadda rundunar Al-Qassam ta bayyana a wata sanarwa da ta wallafa a shafin Telegram.

Isra'ila ta kashe dubban mutane a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba. / Hoto: Reuters

1100 GMT — Isra'ila ta kashe manomi a sansanin 'yan gudun hijira

Isra’ila ta kashe wani manomi da kuma ji wa wani rauni a wata gona da ke sansanin ‘yan gudun hijira ta Maghazi a Gaza.

Kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a yau Lahadi.

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga kwana na uku na yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni tsakanin Falasdinawa da kuma Isra’ila.

1045 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyu a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun kara kashe Falasdinawa biyu a garuruwan Nablus da Jenin da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta tabbatar.

Isra'ila da Falasdinawa sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni ta kwanaki hudu. / Hoto: Reuters

Ma'aikatar Lafiyar ta ce a cikin sa'o'i 24, akalla Falasdinawa bakwai dakarun na Isra'ila suka kashe a cikin sa'o'i 24 a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ta shiga kwana na uku.

A bangare guda kuma, gidan fursunan Isra'ila ya ce ya karbi jerin sunayen Falasdinawa 39 wadanda ake sa ran saki a ranar Lahadi, kamar yadda kafar watsa labarai ta Isra'ilar ta ruwaito.

#