Tsawon kwanaki 107, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,105 da raunata mutum 62,681.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe karin mutum 178 a Gaza

1155 GMT — Sojan Isra'ila da ya yi yaki a Gaza ya kashe abokinsa a Tel Aviv

Wani sojan Isra’ila wanda bai jima da dawowa daga yaki a Gaza ba ya kashe abokinsa a Tel Aviv, kamar yadda kafafen watsa labarai na Isra’ila suka bayyana.

Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta bayyana cewa sojan ya bi abokin nasa har gidansa inda ya kashe shi.

Kafafen watsa labaran Isra’ila a cikin ‘yan kwanakin nan sun ruwaito cewa akwai dubban sojoji wadanda suka je yaki Gaza suka dawo da ke fuskantar matsalar kwakwalwa.

1139 GMT — Isra'ila ta kashe karin mutum 178 a Gaza

Isra'ila ta kashe karin Falasinawa 178 da kuma raunata 293 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya da ke Gaza ta tabbatar.

Ko a jiya Asabar sai dai ma'aikatar ta ce sojojin na Isra'ila sun kashe 165 tsakanin Juma'a zuwa Asabar.

Zuwa yanzu Isra'ila ta kashe Falasdinawa 25,105 da kuma raunata 62, 681 tun daga 7 ga watan Oktoba.

#