Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 58 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falaadinawa fiye da 15,207, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 40,000 sun jikkata.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe kananan yara da mata a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

0444 GMT — Isra'ila ta kashe kananan yara da mata a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

Jiragen yakin Isra'ila sun kai jerin hare-hare a sassa dabna-daban na Gaza, inda suka kashe mutane da dama ciki har da mata da kananan yara, kamar yadda Ma'aikatar Cikin Gida ta yankin ta bayyana.

Hare-haren sun fi mayar da hankali ne a al Burij, Dier al Balah, da kuma wasu yankuna da ke gabashin Rafah.

Alkaluman mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun karu zuwa 15,207, sannan wadanda suka jikkata sun zarta 40,652. Jami'ai sun yi amannar cewa dubban gawawwaki na binne a cikin baraguzan gine-gine sakamakon hare-haren Isra'ila.

Kazalika, Isra'ila ta kaddamar da jerin hare-hare ta sama a Gabar Yamma da Kogin Jordan, abin da ya kara tayar da hankula a yankin.

#