Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 58 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falaadinawa fiye da 15,207, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 40,000 sun jikkata.
1345 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 700 a kwana guda a Gaza
Ofishin watsa labarai na Falasdinu a Gaza ya bayar da rahoton cewa hare-hare ta sama da Isra’ila ke kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar sama da mutum 700 a sa’o’i 24 da suka gabata.
Makarantar “Holy Family” wadda ke kasancewa a matsayin mafaka ga wadanda suka rasa muhallansu, ta zama daya daga cikin wuraren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa hari a birnin.
A Gabar Yamma da Kogin Jordan kuwa, Isra’ila ta bayar da umarnin rushe wani gini a unguwar Al Sawana da ke Gabashin Birnin Kudus wanda a ginin ne mai wa’azi a Masallacin Al Aqsa Sheikh Ikrimah Sabri yake tare da wasu iyalai.
0426 GMT — WHO ta bukaci a 'tsagaita wuta' a hare-haren Gaza
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana matukar kaduwa game da luguden wutar da Isra'ila take yi a Gaza.
Tawagar WHO da ke yankin ta ziyarci Asibitin Nassar da ke kudancin Gaza ranar Asabar, inda ta bayyana mawuyacin halin da mutane suke ciki.
Asibitin, wanda mutane suke tururuwar zuwa domin kula da lafiyarsu, yana aiki fiye da sau uku na yadda ya kamata abin da ya jefa shi cikin mawuyacin hali.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya wallafa sako a shafinsa na X inda ya bayyana mawuyacin halin da ake ciki a yankin, yana mai cewa fiye da "majiyyata 1,000 ne suke cikin asibit — adadin da ya zarta yadda ya kamata ya yi aiki har sau 3. Mutane da yawa na neman matsuguni a asibitin, inda suka cika shi makil."
Asibitin Nassar ya yi cikar da ba zai iya kula da marasa lafiya, inda yanzu ake kwantar da marasa lafiya a dandarin kasa inda suke cikin azaba.
0444 GMT — Isra'ila ta kashe kananan yara da mata a sabbin hare-haren da ta kai Gaza
Jiragen yakin Isra'ila sun kai jerin hare-hare a sassa dabna-daban na Gaza, inda suka kashe mutane da dama ciki har da mata da kananan yara, kamar yadda Ma'aikatar Cikin Gida ta yankin ta bayyana.
Hare-haren sun fi mayar da hankali ne a al Burij, Dier al Balah, da kuma wasu yankuna da ke gabashin Rafah.
Alkaluman mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza sun karu zuwa 15,207, sannan wadanda suka jikkata sun zarta 40,652. Jami'ai sun yi amannar cewa dubban gawawwaki na binne a cikin baraguzan gine-gine sakamakon hare-haren Isra'ila.
Kazalika, Isra'ila ta kaddamar da jerin hare-hare ta sama a Gabar Yamma da Kogin Jordan, abin da ya kara tayar da hankula a yankin.
A unguwar Qalqilya, dakarun Isra'ila sun kashe wani matashi dan shekara 21 sannan suka jikkata wasu mutane da dama. Hakan ya sa an sanya ayyana gudanar da gagarumar zanga-zanga a Qalqilya, abin da ya tayar da jijiyoyin wuya a yankin na Falasdinu.