Luguden wutar da Isra'ila ta kwashe kwana 76 tana yi a Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 20,000, da jikkata fiye da 52,600.
0819 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa fiye da 50 a Gaza a awa 24
Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 55 hare-haren da ta kai Khan Younis a kudancin Gaza a awa 24 da suka gabata, a cewar kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasdinu.
Khan Younis shi ne birni mafi girma a kudancin Gaza inda mutum kusan 400,000 suke zaune kafin Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza.
Duk da cewa Isra'ila ta bai wa mazauna arewacin Gaza umarni su koma kudanci, abin da ke nuna cewa kudancin Gaza na da kwanciyar hankali, amma Isra'ila ta fadada hare-hare ta kasa da sama a kudanci, lamarin da ya raba miliyoyin mutane daga muhallansu.
0525 GMT —An kashe karin sojojin Isra'ila a yakin Gaza
Hukumar Watsa Labarai ta Isra'ila ta bayar da rahoton kashe karin sojojin kasar uku da ji wa guda takwas munanan raunuka a Gaza.
Rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kisan sojojin, cikinsu har da Kofur Lavi Ghasi, a yayin da adadin sojojin Isra'ila da aka kashe a Gaza ya kai 469 tun ranar 7 ga watan Oktoba.
Rundunar sojin ta Isra'ila ta fitar da wata sanarwa da ke cewa an kashe Kofur Lavi Ghasi (Mai shekara 19) daga Bataliya ta 931 da ke Birged Nahal a yakin da ake yi a arewacin Gaza.
Sanarwar ta kara da cewa an kashe Laftanar Yaacov Elian ( Mai shekara 20) da Laftanar Omri Shwartz (Mai shekara 21) na Bataliyar Gefen yayin gumurzu a arewacin Gaza.
Rundunar Sojin Isra'ila ta bayyana cewa an ji wa sojojinta takwas munanan raunuka a gwabzawar da suka yi a Gaza.
0119 GMT — Isra'ila ta bai wa kashi 20 na Falasdinawan da ke Khan Younis wa'adi
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Isra'ila ta fitar da wani sabon wa'adi, inda ta umarci mazauna yankunan babban birnin Gaza da aka yi wa ƙawanya da su gudu.
Ofishin kula da ayyukan jinƙai na MDD, OCHA, ya ce Isra’ila ta fitar da taswirori da ke nuna sabbin wuraren da suka shafi kusan kashi 20 cikin 100 na birnin Khan Younis da aka yi wa ‘yan gudun hijira.
Kafin faɗan ya barke, yankin na da mutane sama da 110,000, in ji OCHA.
Ya kuma ƙara da cewa yankin ya hada da matsuguni 32 da ke dauke da ‘yan gudun hijira sama da 140,000, wadanda akasarin su a baya sun yi gudun hijira daga arewa.
0003 GMT — Isra'ila ta tsare Falasdinawa 300 daga Gaza cikin mawuyacin hali
Kafofin watsa labaran Isra'ila sun rawaito cewa sojojin kasar na tsare da daruruwan Falasdinawa daga yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya, ana zarginsu da kasancewa 'yan kungiyar Hamas reshen rundunarta masu dauke da makamai, a cikin mawuyacin hali.
Tashar talabijin ta Isra'ila ta Channel 12 ta yi zargin cewa a halin yanzu dakarun Al Qassam Brigades 300 ne ake tsare da su a Isra'ila.
Ya ce ana rarraba Falasdinawan rukuni-rukuni, ya danganta da girman matsayin mutum - da irin haɗarinsa.
An yi nuni da cewa, an kama su ne a garuruwa da yankunan da ke kusa da Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma ana zarginsu da hannu a rikicin Hamas.
Tashar ta kara da cewa ana ɗaure su ne duka a cikin kurkukun duhu, kuma ana barin su su fita sau daya don yin wanka.
Ta ce a halin yanzu Isra'ila ba ta da niyyar gurfanar da su a gaban ƙuliya, saboda tsoron kar a cutar da Isra'ilawa da ke tsare a Gaza.
Tashar ta yi nuni da cewa, ana tsare da Falasdinawa a wani wurin da ke karkashin kulawar hukumar kula da gidajen yarin Isra’ila, kuma an raba su da sauran fursunonin da ke gidajen yarin Isra’ila.
2240 GMT — Sama da sojojin hayar Faransa 4,000 ne suka shiga yakin Isra'ila a Gaza
Wani dan majalisar dokokin Faransa ya buƙaci gwamnatin kasar da ta binciki ‘yan kasar sama da 4,000 da ke yaƙi tare da sojojin Isra’ila da suka mamaye kasar, kan laifukan yaƙi a yankunan Falasdinu.
Thomas Portes daga jam'iyyar La France Insoumise [LFI] ya rubuta a kan X cewa ya aika da wasiƙa ga Ministan Shari'a Eric Dupond-Moretti, yana neman a gudanar da bincike kan sojojin Faransa 4,185 da ke yaƙi tare da sojojin Isra'ila a Gaza.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci Isra’ila da kada ta “dakatar da Gaza” ko kuma ta kai hari ga farar hula ba gaira ba dalili.
Da yake jadada cewa ya kamata Faransa ta yi adalci wajen yi wa sojojin hukunci idan aka same su da aikata laifukan yaƙi, Portes ya ce zai daukaka ƙara zuwa ofishin mai gabatar da kara.
Portes ya ce ba za a amince da shigar 'yan kasar Faransa cikin laifukan ba, idan aka yi la'akari da laifukan yaki da sojojin Isra'ila ke aikatawa a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Wasu kungiyoyi da dama ne suka bayyana damuwar tun da farko, ciki har da kungiyar Faransa Palestine Solidarite [AFPS], wacce ta fitar da wata sanarwa da ta bukaci a dauki matakin hukunta ‘yan kasar Faransa da ke da hannu a laifukan yaki.