Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
1056 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 47 da safiyar Lahadi, daga ciki har da 'yan gudun hijira
Falasdinawa akalla 47 aka bayar da rahoton cewa Isra’ila ta kashe a wasu hare-haren sama da aka kai a birnin Jabalia da sansanin ‘yan gudun hijira na Deir Al-Balah a Zirin Gaza, kamar yadda kafar watsa labaran Falasdinu ta ruwaito.
“Falasdinawa 35 aka kashe gommai kuma suka samu rauni a ranar Lahadi a lokacin da Isra’ila ta tayar da bam a wani gida da ke birnin Jabalia a arewacin Zirin Gaza,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ya ruwaito.
Wasu mazauna yankunan sun tabbatar da cewa akwai wasu mutum 90 wadanda aka raunata wasu kuma na karkashin baraguzai.
"Jirigin yakin Isra'ila ya kuma kai hari wani gida da ke sansanin 'yan gudun hijira na Deir al-Balah wanda ke a tsakiyar Zirin Gaza, inda ya halaka akalla mutum 12 da raunata gommai, wadanda akasarinsu jama'ar da a baya suka rasa muhallansu ne," kamar yadda hukumar ta bayyana.