Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
1305 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 17 a kusa da wani asibiti
Akalla Falasdinawa 17 Isra’ila ta kara kashewa a harin da ta kai ta sama a kusa da Asibitin Yousef El Najar da ke kudancin Gaza, kamar yadda wadanda suka shaida lamarin suka tabbatar.
Jiragen yaki sun kai hari kan gidaje biyu da ke kusa da asibitin a birnin Rafah, kamar yadda shaidu suka tabbatar.
“Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan gidajen da asuba, inda suka yi babbar barna a yankin,” kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
0925 GMT — Hamas ta musanta rahoton musayar fursunoni tsakaninta da Isra'ila
Wani babban jagoran Hamas ya musanta rahotannin da ke cewa kungiyar ta Hamas ta cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da Isra’ila.
“Rahotanni kan batun musayar fursunoni ba gaskiya bane,” in ji Izzat al Rishq a wata sanarwa da ta fitar.
Haka kuma wasu jaridun Isra’ila sun musanta wannan zargin na musayar fursunoni. “Babu komai har yanzu,” kamar yadda jaridar Post ta Birnin Kudus ta ruwaito jami’in na Isra’ila yana cewa.
0425 GMT — Isra'ila ta yi luguden wuta a Asitibin Indonesia da ke arewacin Gaza, ta kashe mutane da dama
Falasdinawa akalla takwas ne suka mutu yayin da gomman suka jikkata sakamakon luguden wuta da aka Isra'ila ta yi da makamai masu linzami a Asibitin Indonesia da yankunan da ke kusa da shi a areacin Gaza, a cewar wasu majiyoyi na asibitin,, baya ga bude wuta da Isra'ila ta yi kan duk mutumin da ya yi yunkurin fita daga asibitin.
Majiyoyin sun kara da cewa dakarun Isra'ila sun yi ta barin wuta a hawa na biyu na asibitin, lamarin da ya sa wurin ya lalace baki daya, sannan ta jikkata likitoci biyu a yayin da suke aiki.
Sun kara da cewa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe yayin harin yana karuwa, musamman bayan da ta katse wutar lantarki don haka yana da matukar wahala a iya yi wa mutane tiyata don ceto rayukansu.
Ganau sun ce hare-haren na Isra'ila sun sa wutar lantarkin asibitin ta katse bayan janaretocinta sun daina aiki.
1222 GMT — An kwashe bakwaini daga Asibitin Al Shifa yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa Gaza hari
Akalla jarirai bakwaini 31 aka kwashe daga babban asibitin Gaza, kuma za a kai su Masar, in ji jami’an kiwon lafiya na Falasdinu, yayin da wasu da dama da suka samu munanan raunuka ke nan a makale a wurin kwanaki bayan da sojojin Isra’ila suka mamaye harabar.
Kakakin ma'aikatar lafiyar Medhat Abbas ya tabbatar da kwashe jarirai 30. Hukumar agajin agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce ta kwashe jarirai 31 tare da hadin gwiwar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Ta ce za a kai su asibitin da Hadaddiyar Daular Larabawa ke kula da shi a birnin Rafah da ke kan iyakar Masar.
1902 GMT — Ministan Isra'ila ya nemi kasashen duniya 'su samar wa Falasdinawa matsugunai a wasu wuraren'
Wani ministan Isra'ila ya ce bai kamata kasashen duniya su bayar da kudade don sake gina yankin Gaza da Isra'ila ta lalata ba, maimakon haka gara su samar "da matsugunai bisa radin kai" ga Falasdinawa a fadin duniya.
Ministan leken asirin Isra'ila Gila Gamliel ya ce "zabi" daya bayan an gama yaƙin shi ne "samar da shirin sake tsugunar da Falasdinawa ta hanyar gina musu matsugunai bisa taimakon sa kai, saboda dalilai na jinƙai, a wajen Zirin Gaza.
A rubutun da ya yi a jaridar The Jerusalem Post, ya ce "maimakon a ba da kudi don sake gina Gaza ko kuma ga kungiyar UNRWA da ta gaza, kasashen duniya za su iya taimakawa wajen dakar nauyin sake tsugunar da jama'ar Gaza, tare da taimakawa al'ummar Gaza gina sabbin matsugunai a sabbin kasashen da suka karbi bakuncinsu."
"Hakan zai iya zama mafita ta nasara: nasara ga fararen hula na Gaza da ke neman rayuwa mafi kyau da nasara ga Isra'ila bayan wannan mummunan bala'i."
Hukumomin Falasdinu a Gaza da yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, sun sha yin watsi da irin wadannan shawarwarin da jami'an Isra'ila ke bayarwa, suna masu cewa hakan kabilanci ne da kuma son kawar da al'ummar Falasdinawa.
1920 GMT — An sake kaseh 'yan jarida uku a hare-haren Is'ila a Gaza
An kashe shugaban wata fitacciyar cibiyar yada labarai a Gaza da wasu 'yan jarida biyu a karshen makon nan a hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin, in ji 'yan uwansu, lamarin da ya ƙara yawan 'yan jarida da suka mutu a rikicin na makonni shida.
Kwamitin Kare 'Yan Jaridu (CPJ) mai hedkwata a birnin New York ya ce idan aka hada adadin wadanda suka mutu a karshen makon a yanzu yawan ƴan jaridan da suka mutu ya kai 48, tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Kungiyar ta CPJ, wadda jerin sunayen da ta fitar ya kunshi ‘yan jaridun da aka kashe a bangarorin biyu na rikicin, duk da yake dai akasarin su a Gaza ne, ta ce takan nemi akalla majiyoyi biyu don tabbatar da kowace mutuwa.
Ta ce jerin sunayen wadanda aka kashe sun hada da Falasdinawa 43 da Isra’ilawa hudu da kuma dan Lebanon daya.