Tsawon kwanaki 113, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 26,257 da raunata mutum 64,797.
1356 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 174 a Gaza da raunata 310
Akalla Falasɗinawa 174 Isra’ila ta kara kashewa sannan ta raunata 310 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar.
“Ƴan Isra’ila masu kama wuri zauna sun yi kisan kiyashi kan iyalai 18 a Zirin Gaza, inda mutum 174 suka rasu tare da raunata 310 a sa’o’i 24 da suka gabata,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa.
“Akwai mutane da dama da har yanzu sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai da kan tituna yayin da masu aikin ceto suka gaza kaiwa gare su,” in ji sanarwar.