Yaƙin da Isra'ila ta  kwashe kwana 274 tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 38,011 — kashi 70 daga cikinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum 87,445, yayin da mutum fiye da 10,000 ke danne a ɓaraguzai, kana ta sace mutum aƙalla 9,500.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 11 a Gaza

0515 GMT — Hare-haren jiragen Isra’ila maras matuƙa sun faɗa kan wurare da dama a Birnin Gaza da sansanonin gudun hijira na Maghazi da Nuseirat inda suka yi sanadin mutuwar aƙalla farar hula 11 da kuma jikkata wasu da dama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya sanar.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa mutum tara ne suka mutu a lokacin da sojojin na Isra’ila suka kai hari a wani gida da kuma wurin ajiye kayayyaki na hukumar UNRWA a Maghazi da Nuseirat.

Haka kuma majiyoyi sun tabbatar da kashe farar hula biyu a harin da Isra’ila ta kai kan wani gini a cikin Birnin Gaza.

2226 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama, cikinsu har da mata, tare da jikkata gommai a jerin hare-hare da ta kai a faɗin yankin Gaza.

Ma'aikatan lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency, cewa an kai gawawwakin mutum bakwai Asibitin Al-Awda da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Gaza, bayan Isra'ila ta yi luguden wuta a wani gida na iyalan Abu Owemer.

Sojojin Isra'ila sun ci gaba da yin luguden wuta a yankin Shejaiya da ke gabashin Birnin Gaza, inda suka lalata gidaje da dama, kamar yadda wata majiya ta gaya wa Anadolu.

Kazalika wata majiya a Asibitin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza, ta ce Isra'ila ta kashe mutum guda sannan ta jikkata da dama a hare-hare ta sama da jiragenta suka kai yankin Bani Suhaila na gabashin Khan Younis.

Haka kuma Isra'ila ta kashe wani mutum guda a Rafah a yayin da yake taimaka wa motocin da ke ɗauke da kayan agaji da ke wucewa ta yankin, in ji majiyoyin da ke asibitin yankin.

Da ma dai Isra'ila ta daɗe tana kai hari kan ma'aikatan da ke taimaka wa motocin kayan agaji da 'yan sanda, inda ta kashe gommai.

2100 GMT — Sojojin Isra'ila sun kakkaɓo rokokin da aka harba daga Lebanon zuwa Galilee

Rundunar sojoji Isra'ila ta ce ta kakkaɓo ƙarin rokoki da aka harba daga kudancin Lebanon inda suka nufi yankin Galilee da ke arewacin Isra'ila a yayin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya tsakaninta da mayaƙan Hezbollah.

Wata jaridar Isra'ila mai sunaYedioth Ahronoth ta ambato rundunar sojin tana cewa an harba rokoki goma daga kudancin Lebanon inda suka nufi yankin Margaliot.

Jaridar ta ƙara da cewa sojojin sun mayar da martani ta hanyar kai hari a yankunan da aka harbo makaman.

Wata sanarwa da Hezbollah ta fitar ta ce mayaƙanta sun harba rokoki samfurin Katyusha zuwa yankin Margaliot domin yin raddi kan hare-haren da Isra'ila take kai wa ƙauyuka da garuruwan da ke kudancin Lebanon.

#