Isra'ila ta kashe Falasdinawa 14, 854 a hare-haren da ta kwashe kwana 49 tana kaiwa a Gaza. Fiye da Falasdinawa 7,000 sun bata ko kuma an binne su a cikin baraguzan gine-gine, a cewar hukumomi.
0420 GMT — Isra'ila ta kai hari wata makarantar MDD, ta kashe mutum 300 da jikkata 100
Akalla mutum 30 sun mutu sannan sama da mutum 100 sun jikkata sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai a wata makaranta da Majalisar Dinkin Duniya ke gudanarwa a arewacin Gaza, a cewar kungiyar Hamas mai fafutukar kare hakkin Falasdinawa.
An kai harin ne a Makarantar Abu Hussein wacce hukumar UNRWA ke gudanarwa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia, a cewar Hamas.
Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai kan wannan batu ba.
0400 GMT — Isra'ila ta kai harin bama-bamai a Asibitin Indonesia da ke Gaza
Dakarun Isra'ila sun kai harin bama-bamai a Asibitin Indonesia da ke arewacin Gaza inda suka lalata inijinin da ke ba shi wutar lantarki, a cewar Ma'aikayar Kiwon Lafiya ta yankin.
"An yi luguden wuta a kan injinin samar da hasken lantarki da kuma babban ginin asibitin," a cewar kakakin ma'aikatar Ashraf al Qudra a wata takaitacciyar sanarwar da ya fitar.
"Rayuwar majinyata 200 da ma'aikatan asibitin na cikin hatsari a yayin da ake ci gaba da kawo hari," in ji shi.
Isra'ila ta ka harin ne gabanin shigar lokacin tsagaita wuta tsakaninta da Hamas ranar Juma'a da misalin karfe 7 na safe a agogon kasar wato karfe 5 a agogon GMT.
Hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a Gaza tun 7 ga watan Oktoba sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 14,854, ciki har da kananan yara 6,150 da mata 4,000, a cewar hukumomin yankin.
A nata bangaren, Isra'ila ta ce an kashe 'yan kasarta 1,200.