Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,313 da jikkata mutum 57,296 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin.
1011 GMT —Isra'ila ta kai hari a ofishin kungiyar Palestinian Red Crescent
Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a ginin kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent Society (PRCS) inda suka kashe mutum guda tare da jikkata mutum shida.
Kungiyar ta wallafa bidiyo da ya nuna cewa harin ya sauka a gininta da ke birnin Khan Younis.
Kungiyar ta PRCS, wadda ke bayar da agajin magunguna da na jinkai, ta fuskanci hare-hare a yakin da Isra'ila ta kaddamar a Gaza.
Kazalika Isra'ila ta kashe Falasdinawa 14, ciki har da kananan yara tara, a jerin hare-haren da ta kai a yammacin birnin Khan Younis na Gaza, a cewar ma'aikatar kiwon lafiya ta yankin.
0150 GMT —Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin tan 65,000 a 'yakin kare-dangi' na Gaza
Sojojin Isra'ila sun yi harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da luguden bama-ba masu nauyin sama da tan 65,000 tonnes a yakin da take yi a Gaza, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gwamnatin Gaza.
"Jiragen yakin sojoji mamaya sun harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da manyan bama-bamai, wasu daga cikinsu na da nauyin tan dubu biyu, a hare-haren kare-dangi na yakin da suka yi a Zirin Gaza, kuma da gangan suke kai hari kan gidaje," in ji ofishin.
"Nauyin bama-baman da sojojin suka harba a Zirin Gaza ya zarta tan 65,000, wanda ya fi nauyin bama-baman nukiliya guda uku da aka jefa a birnin Hiroshima na kasar Japan."
Ofishin ya ce kusan kashi "biyu cikin uku na bama-bamai da makamai masu linzamin...ana harba su ne a ko'ina ba tare da kiyaye kowanne wuri ba."
0100 GMT — Wani jami'in gwamnatin Biden ya ajiye aiki saboda goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra'ila
Wani jami'i a Ma'aikatar Ilimi ta Amurka ya ajiye mukaminsa saboda yadda Shugaba Joe Biden yake goyon bayan Isra'ila a luguden wutar da take yi a Gaza da ta mamaye, wata alama da ke nuna rabuwar kawuna a gwamnatin kasar.
Tariq Habash, mataimakin na musamman a fannin Tsare-Tsare na Ma'aikatar Ilimi, a wata wasika da ya aike wa Sakataren Ilimi Miguel Cardona, ya ce: "Ba zan iya ci gaba da yin gum da bakina ba a yayin da gwamnati ta rufe idanunta game da hare-haren da ake kai wa Falasdinawa da ba su da laifi, abin da masu kare hakkin dan'adam suka bayyana a matsayin kisan kare-dangi da gwamnatin Isra'ila ke yi."
"Ba zan kasance cikin masu aikata laifi a yayin da wannan gwamnatin ta gaza yin amfani da matsayin wajen hana babbar kawarta Isra'ila ci gaba da cin zarafi a Gaza tare da katse hanyoyin samun abinci da ruwa da lantarki da fetur da magunguna, lamarin da ya haddasa cutuka da yunwa," in ji Habash.