Hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza da aka yi wa ƙawanya - wanda yanzu haka ya shiga rana ta 206 - ya kashe Falasdinawa akalla 34,488 tare da raunata wasu 77,643 yayin da ake ci gaba da kira ga Firaministan Isra'ila Netanyahu da ya sauka daga mulki.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Lebanon

1407 GMT –– Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Lebanon

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a kudancin Lebanon a daidai da ake ƙara samun rashin jituwa tsakanin ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da ƙasar.

Isra'ila ta kai harin makaman atilari a garuruwan Ayta ash-Shaab da Alma ash-Shaab da Naqoura, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar Lebanon ya ruwaito.

Haka kuma rahotanni sun ce Isra'ilar ta kai hare-hare ta sama a kan garuruwan Tyre Harfa da Maroun al-Ras da Naqoura da Blat.

Babu wani ƙarin bayani dangane da waɗanda suka samu rauni sakamakon harin.

#