Tsawon kwanaki 130, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,473 da raunata mutum 68,146.

KAI TSAYE: Isra'ila ta ji wa wakilan Al Jazeera  biyu 'mummunan rauni'

1251 GMT — Isra'ila ta ji wa wakilan Al Jazeera biyu 'mummunan rauni'

Kafar watsa labarai ta Al Jazeera a ranar Talata ta ce an raunata ƴan jaridarta biyu a wani hari da Isra’ila ta kai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.

Kafar watsa labaran ta ƙasar Qatar ta ce rayuwar wakilinta Abu Omar na cikin hatsari sakamakon an yanke ƙafarsa ta dama.

Haka kuma akwai wani wakilinta mai ɗaukar hoto Ahmad Matar wanda ya samu rauni mai yawa tare da zubar da jini. A ƴan kwanakin nan Isra’ila na zafafa hare-hare a birnin Rafah wadda ke kan iyaka da ƙasar Masar.

#