Hare-haren da Isra'ila ta kwashe 68 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,412, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 50,100 sun jikkata kana dubban na binne a karkashin baraguzan gine-gine

KAI-TSAYE: Isra'ila ta ce an kashe karin sojojinta takwas a arewacin Gaza

0715 GMT — Isra'ila ta ce an kashe karin sojojinta takwas a arewacin Gaza

Rundunar sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da cewa an kashe karin sojojinta takwas, ciki har da kwamandoji a arewacin Gaza a sa’o’i 24 da suka gabata.

Rundunar sojin ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar.

Kafar watsa labarai ta Isra’ila KAN ta sanar da cewa daga cikin sojojin na Isra’ila da aka kashe har da Laftanar Kanal Tomer Grinberg mai shekara 35 da Manjo Moshe Avram da Roei Meldasi mai shekara 23 wadanda duka kwamandoji ne.

0023 GMT — Australia ta goyi bayan kudurin MDD na tsagaita wuta a Gaza a ra'ayin da ya sha bamban da Amurka

Ministar harkokin wajen Australia Penny Wong, ta ce kasar ta goyi bayan wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci a tsagaita wuta a Zirin Gaza, saboda nuna damuwa ga fararen hula a yankin da aka yi wa ƙawanya, a wani ra'ayi da ya jawo rabuwar kai da babbar ƙawarta Amurka.

Bayan gargadin da jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka yi game da ta'azzarar ƙazamin rikicin jinƙai a Gaza a yakin da Isra'ila ta kwashe watanni biyu ana yi a can, MDD mai wakilai 193 ta amince da ƙudurin tsagaita wuta inda ƙasashe 153 da suka hada da Australia suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsagaita wutar, inda 23 kuma suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri'ar.

Kasashe goma ne suka kada kuri'ar ƙin amincewa da tsagaita wutar kuma sun haɗa da Amurka da Isra'ila.

Wong ya shaida wa wani taron manema labarai a Adelaide bayan da MDD ta zartar da kudurin cewa, Australia ta ci gaba da tabbatar da hakkin Isra'ila na kare kanta. "Kuma a yin haka, mun ce dole ne Isra'ila ta mutunta dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa, dole ne a kare fararen hula da kayayyakin aikin farar hula, ciki har da asibitoci.

"Kudurin da muka goyi bayan ya yi daidai da matsayin da muka zayyana a baya kan wadannan batutuwa."

0153 GMT — Jajircewar Falasɗinawa ta sa Biden ya gane yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza "hauka ne" : Hamas

Juriya da tsayin daka na al'ummar Falasdinu ya sa shugaban Amurka Joe Biden ya fahimci "haukar" sojojin Isra'ila a mamayar da suke yi a Gaza, in ji wani babban shugaba a Hamas.

Osama Hamdan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a birnin Beirut a lokacin da aka tambaye shi game da wani sharhi da kamfanin Biden ya yi a safiyar ranar cewa Isra'ila na rasa goyon bayanta a duniya.

Harin na Isra'ila "zai haifar da mummunan sakamako" kan Isra'ila da kuma yiwuwar sake zaben Biden, in ji shi.

Ya yi nuni da cewa akwai saɓani ƙarara a cikin kalaman na Biden, yana mai cewa a jiya ya tabbatar da cikakken goyon bayansa ga Isra'ila kuma a yau ya bayyana cewa Isra'ila ta fara rasa goyon bayan kasashen duniya.

Biden ya ce gwamnatin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na rasa goyon bayanta a duniya kuma "dole ne Netanyahu ya ƙarfafa tare da sauya" gwamnati don "nemo mafita ta dogon lokaci kan rikicin Isra'ila da Falasdinu."

#