A yau yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 308, inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 39,699 — mafi yawansu mata da yara — ya kuma raunata sama da mutum 91,722. Ana ƙiyasin fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa.

Kai-tsaye: Isra'ila ta ƙaddamar da 'hari' a Khan Younis

Juma'a, 9 ga watan Agustan 2024

0644 GMT — Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da "hare-haren soji" a Khan Younis da ke kudancin Gaza.

Wata sanarwa da runduar ta fitar ta yi iƙirarin cewa ta kai hare-haren ne bayan ta samu wasu bayanan sirri da ke nuna cewa akwai "kayan aikin ƙungiyar Hamas da Islamic Jihad a kudancin Zirin Gaza".

A baya, Isra'ila ta kai hare-hare a Khan Younis, yankin da ke cike da miliyoyin mutanen da aka tilasta wa barin gidajensu na arewacin Gaza, sakamakon luguden wutar da Isra'ila take yi a can.

0327 GMT — Masar ta yi kira ga ƙasashen duniya su matsa lamba kan Isra'ila don ta daina yaƙi a Gaza

Shugaban Masar Abdel Fattah el Sisi ya yi kira ga ƙasashen duniya su ƙara matsa lamba kan Isra'ila domin ta daina yaƙin da take yi a Gaza.

Ya yi kiran ne a tattaunawar wayar tarho da ya yi da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, a cewar wata sanarwa da ofishin shugaban ƙasar Masar ya fitar.

Sanarwar ta ce Sisi ya jaddada wa Macron irin ƙoƙarin da Masar take yi na samar da "hanyar tattaunawa mai ƙwari" tsakanin ɓangarorin da ke rikicin domin daina yaƙin tare da hana shi watsuwa zuwa sauran sassan yankin.

Ya jaddada muhimmancin matsa lamba domin tabbatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, yana mai cewa ci gaba da yaƙin shi ne "babban dalilin" da ya sa ake zaman ɗarɗar a yankin.

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 60 tare da jikkata ɗaruruwa a hare-haren da suka kai a yankuna daban-daban na Gaza cikin awanni 24 da suka wuce. / Hoto: AA

2037 GMT — Masu shiga tsakani sun gayyaci Isra'ila da Hamas da su ci gaba da tattaunawar sulhu a Gaza

Shugabannin kasashen Qatar da Masar da Amurka sun yi kira ga Isra’ila da Hamas da su ci gaba da tattaunawar gaggawa a ranar 15 ga watan Agusta, ko dai a Doha ko Alkahira, don cike gibin da ya rage a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da ake shirin fara aiwatarwa ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Kasashen uku ne suka bayyana hakan a wata sanarwar hadin gwiwa. Sanarwar ta ƙara da cewa "Lokaci ya yi da za a ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tare da sako wadanda aka yi garkuwa da su da fursunoni."

“Yanzu dai yarjejeniyar tana kan teburi inda kawai bayanan aiwatar da su ya rage a kammala,” in ji su, sun kuma ƙara da cewa “sun shirya gabatar da ƙudurin sulhu na karshe wanda zai warware sauran batutuwan aiwatar da su ta hanyar da ta dace da abin da kowa ke bukata."

Sa'o'i kadan bayan haka, Isra'ila ta ce za ta aike da wata tawaga ta masu shiga tsakani "zuwa wurin da aka amince da su don kammala cikakkun bayanan aiwatar da yarjejeniyar."

Falasdinawa dai na son a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen yakin, yayin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce yaƙinsa na kisan kare dangi zai tsaya a Gaza ne kawai da zarar an fatattaki Hamas - burin da masana da dama ke ganin cewa ba gaskiya ba ne.

Falasdinawa sun ce ta hanyar kashe mai shiga tsakani na Hamas Ismail Haniyeh, Isra'ila ta nuna cewa ba ta da sha'awar sasantawa ko musayar mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma fursunoni.

A yau yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya shiga kwana na 308, inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 39,699 / Hoto: AFP

2100 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 60 a cikin awa 24

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa akalla 60 tare da jikkata wasu daruruwa a sassa daban-daban na Gaza da aka yi wa ƙawanya a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Mahmud Basal, kakakin sashin kare fararen hula a Gaza, ya bayyana a cikin sanarwarsa cewa an kashe wani Bafalasdine sakamakon harin bam da sojojin Isra'ila suka kai a gidan iyalan Reyyan da ke arewacin Gaza.

Jami'an Falasdinawa sun ce an kashe Falasdinawa 26 a hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a arewacin Gaza da birnin Gaza.

Falasdinawa biyar ne suka mutu sakamakon harin da sojojin Isra'ila suka kai wa gidan zuri'ar Seldan da ke tsakiyar birnin Gaza, da kuma wasu biyar a hare-haren da aka kai a unguwar Zeytun, da kuma 16 sakamakon harin da aka kai wa makarantun Ez-Zehra da Abdulfettah da ke gabashin birnin, inda Falasdinawan da suka rasa matsugunansu suke samun mafaka.

#