Isra'ila ta kwashe kwana 279 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,295 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 88,241, kana mutum fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai.

Kai-tsaye: Isra'ila na yin luguden wuta a Birnin Gaza  yayin da masu shiga tsakani ke neman a tsagaita wuta

1013 GMT — Isra'ila na yin luguden wuta a Birnin Gaza yayin da masu shiga tsakani ke neman a tsagaita wuta

Mazauna Birnin Gaza sun maƙale a gidajensu sannan an kasa kwashe gawawwakin mutanen da aka kashe sakamakon luguden wutar da Isra'ila ta ƙaddamar a yankin, a yayin da Washington ke matsa lamba kan a tsagaita wuta a yaƙin da Isra'ila take yi a wajen tattaunawa da ake yi a Masar da Qatar.

Hamas ta ce luguden wutar da Isra'ila take yi a Birnin Gaza City a wannan makon yana iya wargaza yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin.

0441 GMT — Umarnin da Isra'ila ta bai wa Falasɗinawa su fice daga Birnin Gaza 'hauka ne zalla'

Cibiyar bayar da bayanai kan hakkokin ɗan'adam ta Yankunan da Isra'ila ta mamaye, B’Tselem, ta bayyana umarnin da sojojin Isra'ila suka bai wa dukkan Falasɗinawa na ficewa daga Birnin Gaza a matsayin “hauka zalla.”

A wani saƙo da ta wallafa a soshiyal midiya, cibiyar ta yi kira ga ƙasashen duniya su tsoma baki sannan su "nemi Isra'ila ta daina yaƙi nan-take”.

“Bisa ayyukan da Isra'ila take yi, da alama tana da niyyar ci gaba da yaƙi babu ƙaƙƙautawa, inda take lalata gine-gine da kashe mutane ba tare da sanin lokacin da za ta daina ba," in ji saƙon da ƙungiyar ta fitar.

Bisa ayyukan da Isra'ila take yi, da alama tana da niyyar ci gaba da yaƙi babu ƙaƙƙautawa, in ji cibiyar./Hoto: AA

0117 GMT — Amurka tana 'taka-tsantsan' a kan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Amurka tana 'taka-tsantsan' a kan tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, a cewar kakakin Fadar White House kan sha'anin tsaro John Kirby a hira da CNN.

"Muna yin taka-tsantsan game da yadda lamura ke tafiya," in ji Kirby yayin da aka tambaye shi a kan ko tattaunawar tsagaita ta zo ƙarshe.

"Har yanzu akwai babban saɓani tsakanin ɓangarorin biyu. Mun yi amannar cewa za a samu daidaito a kan wannan saɓani, kuma wannan shi ne abin da Brett McGurk da Daraktan CIA Bill Burns suƙe yunƙurin yi a halin yanzu," a cewarsa.

2212 GMT — Erdogan ya gana da Scholz a kan yaƙin Gaza

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz sun tattauna game da yaƙin da Isra'ila take yi a yankin Gaza da ta mamaye.

Erdogan ya shaida wa Scholz cewa dole ne a matsa lamba kan Isra'ila domin ta kawo ƙarshen hare-haren da take kai wa Gaza sannan kada a ɓarar da damar tsagaita wuta, a cewar Daraktan Sadarwa na Turkiyya.

Ya ƙara da cewa yana da matuƙar muhimmanci a ƙara ƙaimi wajen hana yaƙin watsuwa zuwa sauran sassan yankin.

#