Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 60 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 15,899, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 42,000 sun jikkata.

KAI-TSAYE: Isra'ila na duba yiwuwar sakar ruwa cikin gine-ginen karkashin kasa da ke Gaza — WSJ

0038 GMT — Isra'ila na duba yiwuwar sakar ruwa cikin gine-ginen karkashin kasa da ke Gaza — WSJ

Isra'ila ta tattara wasu manya-manyan famfuna da za su malala ruwa cikin gine-ginen karkashin kasa da kungiyar Hamas take amfani da su a Gaza da aka mamaye a yunkurin fatattakarsu daga ciki, kamar yadda jaridarWall Street Journal ta Amurka ta rawaito, inda ta ambato wasu jami'an gwamnatin kasar.

A tsakiyar watan Nuwamba, rundunar sojin Isra'ila ta gama kafa manyan famfuna akalla biyar a wani wuri mai nisan kusan mil daya daga arewacin sansanin 'yan gudun hijira na Al Shati wadanda za su iya sheka ruwa da yawansa zai kai dubban kyubik mita cikin awa daya, domin mamaye dukkan gine-ginen karkashin kasar cikin makonni kadan, in ji rahoton.

Babu cikakken bayani kan ko Isra'ila za ta malala ruwan kafin a saki dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, a cewar labarin. A baya Hamas ta ce ta ajiye dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su a "wurare masu aminci da kuma gine-ginen karkashin kasa."

A lokacin da aka yi masa tambaya game da wannan batu, wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce yana da kyau Isra'ila ta lalata gine-ginen karkashin kasar kuma kasar tana duba hanyoyi daban-daban na yin hakan.

Jaridar Wall Street Journal ta ce wani jami'in Rundunar Tsaron Isra'ila ta Defense Forces [IDF] ya ki cewa uffan kan wannan shiri ko da yake ta ambato shi yana cewa: "Rundunar IDF tana yin aiki domin kawar da ta'addancin Hamas ta hanyoyi daban-daban, inda take amfani da karfin soji da kuma fasahohi."

0123 GMT — Kungiyar bayar da agaji ta Palestine Red Crescent ta daina jin duriyar ma'aikatanta da ke Gaza

Kungiyar bayar da agaji ta Palestine Red Crescent Society ta ce ta daina jin duriyar tawagar likitocinta da ke yankin Gaza da aka mamaye.

Ta bayyana haka ne bayan kamfanin sadarwa na Palestine Telecommunications Company [PalTel] ya ce an katse dukkan sadarwa da intanet a Gaza.

"Mun daina jin duriyar ma'aikatanmu da ke Zirin Gaza sakamakon matakin da Isra'ila ta dauka na katse dukkan kamfanonin sadarwa," in ji wata sanarwa da Red Crescent ta fitar.

#