Hare-haren da Isra'ila ta kwashe sama da wata biyu tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 17,487, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 46,480 sun jikkata.

KAI-TSAYE: Isra'ila na ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza bayan Amurka ta ki amincewa da kudurin

1025 GMT — Isra'ila na ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza bayan Amurka ta ki amincewa da kudurin

Isra’ila ta ci gaba da zafafa kai hare-hare a Gaza bayan Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda zai bayar da dama a tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila take kaiwa Gaza.

Hamas da hukumomin Falasdinu sun yi Allah wadai da wannan matakin na Amurka a daidai lokacin da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa mutum 17,487 suka mutu a Gaza, akasari mata da yara.

Haka kuma wani hari da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Khan Yunis ya kashe mutum shida, inda wasu biyar suka mutu a wani hari na daban a Rafah, kamar yadda ma’aikatar ta tabbatar a ranar Asabar.

#