Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 55 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara. Kimanin mutum 7,000 aka danne a baraguzan gine-gine wadanda Isra'ila ta yi wa luguden wuta, a cewar hukumomi.
0455 GMT — Isra'ila da Hamas sun amince a kara wa'adin tsagaita wuta da kwana daya
Isra'ila da kungiyar Hamas mai rajin kare hakkin Falasdinawa sun amince su tsawaita yarjejeiyar tsagaita zuwa karin kwana daya.
Kazalika sojojin Isra'ila sun ce za a ci gaba da mutunta yarjejeniyar "bisa kokarin masu shiga tsakani na ci gaba da ganin an saki karin mutanen da aka yi garkuwa da su, kuma a kan sharudan da aka yarda da su."
Kasar Qatar wadda ke shiga tsakani ta tabbatar da cewa Isra'ila da Hamas sun amince su tsawaita wa'adin yarjejeniyar.
0200 GMT — An gaya wa mayakan Hamas su sanya damara don ci gaba da yaki
Kasashen duniya na matsa lamba kan Isra'ila da Hamas domin su tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta bayan sun yi musayar karin fursunoni sannan an bar karin kayan agaji sun shiga yankin Gaza da aka mamaye.
Sai dai "Majalisar Yaki" ta Isra'ila ta kammala taronta ba tare da cim ma matsaya kan tsawaita yarjejeniyar ba, kamar yadda TRT World ta fahimta. Wasu kafofin watsa labarai na Isra'ila sun ambato majiyoyi suna cewa "jerin sunayen karin mutanen da Hamas ta nemi a sako bai cka sharudan" Isra'ila ba."
Yarjejeniyar tsagaita wutar za ta daina aiki ne da misalin karfe 7 na safe a agogon Gaza, wato karfe 5 a agogon GMT.
Sashen soji na kungiyar Hamas ya shaida wa mayakansa su daura damarar komawa yaki da Isra'ila idan ba a tsawaita yarjejeniyar ba.
"Al-Qassam Brigades yana umartar dakarunsa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a awannin karshe na karewar yarjejeniyar," in ji sanarwar ya fitar. An bukaci mayaka su shiga cikin "damara har sai an fitar da sanarwa a hukumance game da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar," kamar yadda sanarwar ta kara da cewa.
0149 GMT — China ta bukaci a samar da kasashe biyu
China ta yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya wani jadawali da zai kai ga samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu tsakanin Isra'ila da Falasdinu domin kawo karshen rikicinsu.
Ma'aikatar Harkokin Wajen China ce ta gabatar da wannan shawara a rubuce kan rikici Gaza, a yayi da kasar ta karbi jagorancin Kwamitin -- wanda ake yin karba-karba -- a watan Nuwamba.
Akwai bukatar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kara kaimi wurin tattaunawar diflomasiyya da kuma sake duba batun samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu sannan ya hada taron kasashen duniya da zai samar da "kwakkwaran tsari mai amfani" na shawo kan rikicin, in ji takardar da China ta gabatar.
Ta yi kira ga mambobi 15 na Kwamitin su saurari kiraye-kiraye kasashen duniya na tabbatar da tsagaita wuta a yakin.
0155 GMT — Fitacciyar mai fafutuka Ahed Tamimi na cikin Falasdinawa da Isra'ila ta saka
Fitacciyar Bafalasdiniyar nan mai fafutuka Ahed Tamimi na cikin mutum 30 da Isra'ila ta saka a yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da Hamas, a cewar jami'an Isra'ila da na Falasdinu.
A farkon watan nan dakarun Isra'ila suka kama Tamimi, wadda ake yi wa kallon gwarzuwa a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun tana matashiya, bayan an zarge ta da tunzura mutane su yi tarzoma.
Mahaifiyarta ta musanta zargin tana mai cewa an yi shi ne bisa wani sakon bogi a shafukan sada zumunta.
Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ta wallafa sunayen Falasdinawa da ta saka ranar Alhamis da safe a shafinta na intanet ciki har da Tamimi.