Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 55 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara. Kimanin mutum 7,000 aka danne a baraguzan gine-gine wadanda Isra'ila ta yi wa luguden wuta, a cewar hukumomi.
0250 GMT — Isra'ila da Hamas sun amince da tsawaita tsagaita wuta zuwa rana ta takwas - WSJ
Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas sun amince da tsawaita tsagaita wuta zuwa kwana na takwas, a wata yarjejeniya da za ta ƙunshi sakin wasu ƙarin fursunonin Isra’ila da suke tsare a gidan yarin Isra’ilan, kamar yadda gidan jaridar Wall Street Journal ya ambato jami'an Masar suna faɗa.
0250 GMT — Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce motocin agaji 65 ne suka shiga birnin Gaza na arewaci
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bayyana cewa, jimillar manyan motocin agaji 65 ne suka shiga birnin Gaza da kuma arewacin Gaza.
Wannan ya kawo adadin manyan motocin da aka aika zuwa 310 tun bayan da aka dakatar da ayyukan jinƙai a ranar 24 ga Nuwamba.
Sanarwar ba ta yi nuni da ko an aike da motocin man fetur zuwa yankunan biyu ba.
Motoci bakwai dauke da mai da iskar gas sun shiga yankin Zirin Gaza ta kan iyakar Rafah, kamar yadda Wael Abu Mohsen, shugaban sadarwa na bangaren Falasdinawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
0230 GMT — Isra'ila ta kama Falasdinawa 3,390 a Yammacin Kogin Jordan tun ranar 7 ga Oktoba
Sojojin Isra'ila sun tsare Falasdinawa 3,390 a hare-haren da suka kai a yankin Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye tun ranar 7 ga watan Oktoba, ciki har da 260 din da aka kama a lokacin da aka tsagaita wuta, in ji kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyar fursunoni ta Falasdinu da hukumar kula da fursunonin suka fitar, ta ce an kama mutanen ne a cikin gida da kuma wuraren binciken sojoji da suka hada da wadanda aka tilasta musu miƙa wuya sakamakon matsin lamba da kuma wadanda aka yi garkuwa da su.
A ranar Alhamis ne aka kama mutum 30, yayin da adadin wadanda aka kama a ranar Laraba zuwa daren Alhamis ya kai 40, in ji su.
0146 GMT — Wani ɗan Isra'ila da ke tsare a hannun Hamas ya roƙi Netanyahu ya kwaso gawarwakin iyalinsa daga Gaza
Wani ɗan Isra'ilan da ke tsare a hannun ƙungiyar Hamas ya roƙi Firaminista Benjamin Netanyahu ya tsara yadda za a kwaso gawarwakin iyalinsa daga Gaza tare da yi musu jana'iza a Isra'ila, bayan da suka mutu a wani harin sama na Isra'ilan da ta kai yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya a lokacin da suke tsare a wajen Hamas.
Roƙon ya zo ne a cikin wani saƙon bidiyo da rundunar Qassam ta Hamas masu dauke da makamai, ta fitar.
“Bibi [Netanyahu], kun jefa bam tare da kashe matata da ’ya’yana biyu, wadanda su ne abu mafi muhimmanci a rayuwata,” in ji Yardin Bibas.
"Ina roƙonka ka mayar da iyalina zuwa ƙasarsu domin a binne su a Isra'ila, "in ji shi cikin yanayi na tausayi.
“Bibi, ina roƙonka ka mayar da su Isra’ila, don Allah ka dawo da su gida.