Tsawon kwanaki 101, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,968 da raunata mutum 60,582.

KAI-TSAYE: Iran ta nemi a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza

1219 GMT — Iran ta nemi a bi hanyar diflomasiyya don kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza

Ministan Harkokin Wajen Iran ya ce Amurka ba za ta iya yin kira da a yi taka-tsan-tsan ba yayin da take goyon bayan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, yayin da ya yi kira da a warware yaƙin da ake yi ta hanyar diflomasiyya.

Hossein Amirabdollahian, a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da aka watsa ta talabijin tare da takwaransa na Indiya a Tehran, ya yi kira ga jami'an Amurka "ka da su danganta tsaro da muradun Amurka da makomar firaministan Isra'ila da ke faduwa."

0902 GMT Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasdinawa sama da 24,000 a Gaza

Aƙalla mutum 24,100 ne suka mutu a Gaza a cikin tsawon wata uku na mummunan yaƙin da Isra'ila ke yi a yankin da aka yi wa ƙawanya, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasdinu.

Wata sanarwa ta ce yawan wadanda suka mutun ya hada da mutum 132 da aka kashe a cikin awa 24 da suka wuce, yayin da har yanzu akwai mutane da dama da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai, kazalika mutum 60,834 ne suka jikkata tun 7 ga watan Oktoban 2023.

0858 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce akwai wani yaro dan shekara 14 wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon wutar da Isra’ila ta bude a sansanin ‘yan gudun hijira na birnin Jericho.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar WAFA ya bayyana, dakarun na Isra’ila sun harbi yaron a kirji a yayin da suka kai hari sansanin.

0828 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 60 a cikin dare daya

Isra'ila ta kashe sama da Falasdinawa 60 a a cikin dare guda a Gaza a sakamakon hare-haren da take ci gaba da kaiwa, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar.

Ma'aikatar ta bayyana cewa akwai gomman mutane wadanda aka raunata a sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa na atilare a cikin Gaza.

Hare-haren sun fada a cikin biranen Khan Younis da Rafah duka wadanda suke kudanci, da kuma wasu wurare da ke cikin Zirin Gaza, kamar yadda ofishin watsa labaran ya tabbatar.

#