Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 325, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,405 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,468, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000.
Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024
1157 GMT — Iran ta jinjina Hizbullah kan harin da ta kai wa Isra’ila
Iran ta yaba kan hare-haren makami mai linzamai da Hizbullah ta kai wa Isara’ila da jirage marasa matuka, tana cewa Isra’ila ta rasa ikonta na hana irin wadannan hare-haren, a daidai lokacin da ake kara samun tashin hankula a yankin.
A ranar Lahadi shugaban Hizbullah Hassan Nasrallah ya ce kungiyar ta kaddamar da manyan hare-hare kan Isra’ila, inda ta nufi sansanin Glilot – “sansanin tattara bayanan sirri na sojojin Isra’aila mafi girma.”
"Jagororin Isar’ila za su iya boye ko jirkita ko tace wasu bayanai na gaskiya dangane da aikin da Hizbullah ta yi, sai dai ta san cewa ba za a taɓa iya sauya abin da ya faru ba,” kamar yadda mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen iran Nasser Kanani ya wallafa a shafin X.
1056 GMT — Ofishin shugaban Falasɗinawa ya koka kan shirin gina wajen bautar Yahudawa na Ben-Gvir
Ofishin Shugaba Falasɗinawa ya ce kiran da Ministan Isra'ila Gen-Gvir ya yi na a gina wajen bautar Yahudawa a Masallacin Ƙudus yunƙuri ne na jefa yankin cikin wani yaƙin addini da zai tarwatsa komai.
An kashe wani Bafalasɗine a ranar Litinin bayan dakarun Isra'ila sun harbe shi a Gaɓar Yamma da aka mamamye, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinawa.
0254 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Birnin Gaza City da Khan Younis
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama tare da jikkata wasu a harin da ta kai da bama-bamai a gidaje biyu a Birnin Gaza da Khan Younis na yankin Gaza da aka mamaye.
"Mun karɓi gawawwakin shahidai da dama sakamakon luguden wuta da jiragen yaƙin Isra'ila suka yi a wani gida a Layin Al-Shuhada da ke Birnin Gaza," a cewar wani likita a Asibitin Baptist da ke Gaza a hira da Anadolu Agency.
Ganau sun ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a gidan iyalan Abu Rida a garin Abasan al-Kabira da ke gabashin Khan Younis, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.
2104 GMT — Wakilan Hamas sun bar Alƙahira bayan nazari kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Tawagar Hamas da ke cikin tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta bar birnin Alƙahira na Masar bayan ta yi nazari kan sakamakon tattaunawar baya bayan nan da Isra'la daga masu shiga tsakani na ƙasashen Masar da Qatar.
Wani babban jam'i a Hamas Izzat al Rishq, ya wallafa saƙo a Telegram da ke cewa wakilansu "sun bar Masar da maraice bayan sun gana da masu shiga tsakani daga Masar da Qatar da kuma ji daga gare su game da sakamakon baya bayan nan kan tattaunawar tsagaita," ko da yake bai yi cikakken bayani ba.
"Wakilanmu sun buƙaci masu mamaya su yi biyayya ga yarjejeniyar da aka amince da ita ranar 2 ga watan Yuli, kamar yadda yake a cikin shawarwarin Shugaban Amurka Joe Biden da Kwamitin Tsaro na MDD," in ji shi.
Hamas ta jaddada aniyarta "ta aiwatar da jarjejeniyar da aka amince da ita domin cika muradun jama'armu da kuma dakatar da kai musu hari."
Ya ƙara da cewa wakilansu sun "jaddada buƙatar ganin yarjejeniyar ta ƙunshi daina luguden wuta na dindindin, da janyewar Isra'ila daga Gaza da maido da mutane gidajensu da shigar da kayan agaji da sake gina yankin da kuma musayar waɗanda aka yi gakuwa da su."
2216 GMT — Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta karɓi allurai fiye da miliyan 1 na cutar polio
Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta sanar da cewa ta karɓi ruwan allura miliyan 1.26 domin yin rigakafin cutar shan inna.
"A jimilla, allurai miliyan 1.26 na rigakafin OPV2 polio sun iso, tare da robobin ajiye su guda 500," in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar.
"An soma shiri domin ƙaddamar da alluran rigakafin tare da abokan hulɗarmu," a cewar ma'aikatar, ba tare da yin ƙarin bayani ba.