Yaƙin da Tel Aviv ya kwashe shekara ɗaya yana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,065. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ke kai wa a Lebanon tun daga Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,169 kana sun raba fiye da mutum 1.2 da muhallansu.

Kai-tsaye: Indonesia ta ce harin da Isra'ila ta kai ya jikkata ma'aikatanta 2

Juma'a, 11 ga Oktoban 2024

0546 GMT — Indonesia ta tabbatar cewa biyu daga cikin sojojinta masu aikin wanzar da zaman lafiya a ƙarƙashin shirin Majalisar Ɗinkin Duniya sun jikkata a wani hari da Isra'ila ta kai Lebanon, sannan ta ce harin ya keta dokokin ƙasashen duniya.

"A harin da aka kai a wani dogon gini a Nakura, an jikkata jikkata ma'aikatan wanzar da zaman lafiya biyu, kuma 'yan ƙasar Indonesia ne," in ji wata sanarwa da Ministar Harkokin Waje Retno Marsudi ta fitar.

Ta ƙara da cewa an garzaya da mutanen da suka jikkata zuwa wani asibiti.

"Indonesia ta yi Allah wadarai da wannan hari da babbar murya," in ji ta. "Kai hari kan ma'aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da gininta babban keta dokokin Ƙasashen Duniya ne."

0130 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai munanan hare-hare a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da ta mamaye

Jiragen yakin Isra'ila sun harba makamai masu linzami da suka kashe Falasdinawa biyu a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu na WAFA ya rawaito cewa, an kashe 'yan kasar biyu a wani harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai kan wata mota a yankin Jabal al Salihin da ke tsakanin yankin Dhannabah da kuma sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams da ke gabashin Tulkarem.

Majiyoyin sun kara da cewa nan take sojojin Isra'ila suka kai farmaki a yankin bayan sun kai farmakin, inda suka kwashe gawarwakin mutanen, sannan suka janye daga wurin.

Tun da fari da yammacin wannan rana ne sojojin Isra'ila suka kai farmaki kan sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams tare da ƙaƙaba wa sansanin ƙawanya kafin su kai hare-hare.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai munanan hare-hare a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan / Hoto: Reuters

Karin bayani ????

0100 GMT — Manyan jami'an tsaron Isra'ila sun gana a cikin Lebanon

Rundunar sojin Isra'ila ta bayyana cewa, babban hafsan hafsoshin sojin kasar Herzi Halevi da daraktan Shin Bet Ronen Bar sun gudanar da wani bincike na hadin gwiwa a kudancin kasar Lebanon a karon farko.

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce Halevi da Bar "sun gudanar da wani bincike na hadin gwiwa tare da dakarun da ke yaki a kudancin Lebanon, tare da kwamandan rundunar sojojin arewa da kuma kwamandan runduna ta 91."

A cewar jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra'ila, wannan shi ne karo na farko da manyan jami'an tsaro ke gudanar da taro a cikin Lebanon.

#