Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 318, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,099 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 92,609, kana an ƙiyasta cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka rusa.
Litinin, 19 ga watan Agusta, 2024
1020 GMT –– Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ta ce an kashe ma’aikata 207 a Gaza tun 7 ga watan Oktoba
Hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijira a yankin Gabas ta Tsakiya (UNRWA) ta ce an kashe mambobinta 207 a Gaza tun bayan barkewar yakin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
"An kashe 'yan tawagar UNRWA 207 a Gaza tun lokacin da aka fara yakin - ciki har da waɗanda aka kashe a bakin aiki," in ji hukumar a cikin wata sanarwa ta X.
Hukumar ta lura cewa wadanda abin ya shafa ƙwararru ne daban-daban. "Su injiniyoyi ne da malamai,da ma'aikatan lafiya. Ma'aikatan jinƙai ne."
Don girmama waɗannan mutane, UNRWA ta nuna sadaukarwar da suka yi a Ranar Taimako ta Duniya. Sanarwar ta kara da cewa "A ranar taimakon jinƙkai ta duniya da kuma kowace rana muna tunawa da kuma girmama su duka."
0528 GMT — Blinken ya gaya wa Isra'ila cewa Hamas ba za ta yi 'ƙafar-ungulu' ga yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ba.
Wannan lokaci ne "mai muhimmani" a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, in ji Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken a ranar Litinin, inda ya bayyana yunƙurin Washington na baya bayan nan kan ƙulla yarjejeniyar tsagaita tsakanin Isra'ila da Hamas a matsayin "mafi inganci, kuma wataƙila dama ta ƙarshe" ta dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su gida.
Da yake magana kafin ganawarsa da shugaban ƙasar Isra'ila Isaac Herzog, Blinken ya ce Washington na aiki tuƙuru domin ganin ba a ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya ba a Gabas ta Tsakiya a yayin da ake zaman ɗar-ɗar game da yiwuwar martani daga Iran bayan kisan gillar da Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Tehran a watan Yuli.
2213 GMT — Isra'ila ta umarci sojojinta su ƙara ƙaimi wurin kai hare-hare a Gaza
Isra'ila ta yanke shawarar ci gaba da luguden wuta a yankin Gaza da ta mamaye domin ƙara samun dama a shirin tattaunawa ta tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni, in ji wata jaridar Isra'ila da ake wallafawa a shafin intanet.
"Kwanakin baya majalisar tsaron Isra'ila ta bayar da umarni ga sojoji su ƙara ƙaimi a hare-haren da suke kai wa Gaza da zummar ƙarfafa matsayinsu a wajen tattaunawar da ake yi," in ji jaridar Walla, wadda ta ambato wasu majiyoyi na siyasa.
2314 GMT — Biden ya ce har yanzu yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza 'mai yiwuwa ce'
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya yi amanna har yanzu yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza "mai yiwuwa ce".
Har yanzu "ana ci gaba da tattaunawa. Ba za mu karaya ba. Abu ne mai yiwuwa," kamar yadda Biden ya shaida wa manema labarai.
2237 GMT — Sojojin Isra'ila sun jikkata wata Bafalasɗiniya 'yar jarida da ke aika rahotanni daga Gaza
Sojojin Isra'ila sun jikkata wata Bafalasɗiniya 'yar jarida da ke aika rahotanni daga yankin Khan Younis na Gaza da aka mamaye.
Dakarun mamaya na Isra'ila sun yi harbi kai-tsaye kan wata tawagar 'yan jarida, inda suka samu Salma al-Qadoumi a baya, kamar yadda ganau suka shaida wa Anadolu Agency.