Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 324, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,334 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 93,56, kana an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000.

Kai-tsaye: Hezbollah ta harba 'rokoki 320' cikin Isra'ila

Lahadi, 25 ga August, 2024

Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta sanar da harba rokoki 320 cikin Isra’ila, lamarin da ta kira da “matakin farko” na mayar da martani kan kisan da Tel Aviv ta yi wa shugabanta Fuad Shukur.

Sanarwar ta zo ne jim kaɗan bayan sojojin Isra’ila sun kai hari ta sama kudancin Lebanon inda Isra’ilar ta yi iƙirarin ta kai harin ne domin daƙile Hezbollah daga kai mata hari.

Zuwa yanzu babu ƙarin bayani kan ɓarnar da waɗannan rokokin suka yi.

0237 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare Lebanon bayan sojoji sun yi da'awar cewa sun gano Hezbollah na shirin harba wa Isra'ila makaman roka da makamai masu linzami, a cewar sojojin na Isra'ila.

Sojojin na Isra'ila suna ce Hezbollah na "shirin harba makamai masu linzami da rokoki zuwa ƙasar Isra'ila. Domin mayar da martani kan wannan barazana, sojojin Isra'ila sun kai hari kan wasu wurare a Lebanon," a cewar wata sanarwa.

Sojoji sun kuma bai wa mazauna kudancin Lebanon wa'adin su "fice nan-take" a wani saƙo da suka tura da Larabci.

0238 GMT — Isra'ila ta karkatar da jiragen da ke shirin sauka, ta jinkirta tashin wasu a filin jirgi na Ben Gurion na ƙasa-da-ƙasa

Filin jirgi na Ben Gurion na ƙasa-da-ƙasa na Isra'ila ya karkatar da jiragen da ke shirin sauka, ya jinkirta tashin wasu bayan Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Labanon.

2200 GMT — Ise'ila ta kashe Falasɗinawa 63 a sassan Gaza da dama

Aƙalla Falasɗinawa 63 aka kashe aka jikkata da dama a wasu jerin hare-haren Isra'ila ta sama da suka kai sassa da dama na Gaza da aka mamaye.

Asibitin Nasser da ke Khan Younis ya karɓi gawawwakin Falasɗinawa 59.

Mahmoud Basal, mai magana da yawun Hukumar Tsaron Al'umma ta Falasɗinu ya faɗa a wata sanarwa cewa "wasu daga Falasɗinawan da aka kashe a hare-haren na sama na Isra'ila da aka kai gidaje na iyalen Othman ne a Benayen Ain Jalut a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar birnin Gaza."

Ya ƙara da cewa, yankunan da ke gabashin birnin Deir al Balah da sansanin Nuseirat sun fuskanci ruwan makaman atilare na Isra'ila, bayan wa'adin da sojoji suka bayar na ficewa daga yanki mai girma na Deir al Balah a ranar Asabar da yamma.

Basal ya ƙara da cewa "makaman atilare na Isra'ila sun fi yawa a shataletalen Dawla, ya zarce zuwa layi na 8, ya kuma ƙarasa shataletalen Dahdouh (kudu maso yammacin Gaza)."

Ya bayyana cewa sojojin Isra'ila sun "dage wajen tsananin ƙonawa da rusa gine-ginen zama a kudancin Birnin Gaza."

#