Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 354, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,455 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,878 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa.
0413 GMT –– Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta harba makamai masu linzami shida kan sansanonin soji da ke arewacin Isra’ila, daga ciki har da sansanin sojin sama biyu da wani kamfanin haɗa bama-bamai.
Hezbollah ɗin ta ce ta kai wannan harin ne domin mayar da martani kan irin yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta Lebanon ta fitar a Telegram, ta ce ta kai hari kan sansanin sojin sama na Megiddo da ke yammacin birnin Afula sau uku.
Wannan ne karo na farko da ƙungiyar ke kai hari kan sansanin sojin mai nisan kilomita 30 daga iyakar Lebanon.
A wata sanarwar ta daban, ƙungiyar ta tabbatar da cewa ta kai hari kan sansanin sojin sama na Ramat David da kuma Amos, waɗanda sansanoni ne masu muhimmanci na hada-hadar sufuri ga sojojin na Isra’ila.
Haka kuma Hezbollah ɗin ta kai hari wata masana'anta a garin Zichron Ya'acov da ke arewacin birnin Kaisariya, mai tazarar kilomita 60 (mil 37) daga kan iyakar kasar Lebanon, wadda ke samar da ababen fashewa.