Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
1420 GMT — Hezbollah ta ce ta raunata sojojin Isra'ila a kan iyaka
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ce ta kai hari ga sojojin Isra’ila a sansaninsu da ke kusa da kan iyaka inda ta raunata su.
Kungiyar ta Hezbollah na taya Hamas yakin da take yi da Isra’ila.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza inda ta kashe sama da mutum 11,200.
0935 GMT — An binne gawawwaki 179 a cikin kabari guda a harabar asibitin Gaza
Daraktan asibitin Gaza mafi girma a ranar Talata ya ce mutum 179, daga ciki har da jarirai da marasa lafiya wadanda suka mutu a dakin kula da marasa lafiya an binne su a cikin kabari guda a harabar asibitin.
“An tilasta mana rufe su a kabari daya,” in ji daraktan Asibitin Al-Shifa Mohammad Abu Salmiyah inda ya ce akwai jarirai bakwai da marasa lafiya 29 wadanda ke dakin marasa lafiya masu tsananin bukatar kulawa na daga cikin wadanda aka binne.
Wani dan jarida wanda ke a cikin asibitin da ke hadin gwiwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce akwai gawawwaki a ta ko ina a asibitin wadanda suka soma rubewa.
0848 GMT — Isra'ila ta sake kashe Falasdinawa shida a Gabar Yamma da Kogin Jordan
Isra’ila ta sake kashe Falasdinawa shida a hare-haren da take kaiwa cikin dare a Gabar Yamma da Kogin Jirdan da Isra’ilar ta mamaye, kamar yadda kafar watsa labarai ta Falasdinawa ta bayyana a ranar Talata.
Falasdinawa biyar aka kashe a birnin Tulkarem a wani harin sama da Isra’ila ta kai wanda kuma ya raunata mutum tara, inda mutm uku ke cikin hali mai tsanani, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu ya tabbatar.
Haka kuma akwai karin Bafalasdine guda da Isra’ila ta kashe a kusa da birnin Hebron, inda Isra’ilar ta yi ikirarin ya yi niyyar kai musu hari da wuka.
0750 GMT — Lauyoyin Falasdinawa sun shigar da Isra'ila kara a Kotun ICC
Lauyoyin wadanda hare-haren Isra'ila suka fadamawa a Gaza sun shigar da kara a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC da ke birnin Hague na Netherlands.
Wakilin jama'ar Gaza a kotun ICC wato Gilles Devers da wasu mutum hudu da suka masa rakiya domin kai korafin sun bayyana cewa Isra'ila ta aikata laifukan yaki a kan Gaza wadanda suka hada da kisan kare-dangi.
Isra'ila ta kashe sama da mutum 11,180 a Gaza wadanda akasarinsu yara ne tun daga 7 ga watan Oktoba.