Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0123 GMT — 15 Palestinians killed in Israeli air strike targeting house in central Gaza
Aƙalla Falasɗinawa 15 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai wani gida na zuri'ar Abu Shamala a unguwar Zawaida da ke yankin tsakiyar Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya bayyana, yana mai ambato majiyyin watsa labarai.
WAFA ya ce jiragen yaƙi sun kuma kai hari wani gini mai hawa huɗu a unguwar Zaytounda ke kudu maso gabashin Gaza, inda gwamman mutane suka jikkata.
Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren sama babu ƙaƙƙautawa a dukkan yankunan Gaza, lamarin da ke ta jawo mace-mace da jikkata Falasɗinawa.
0150 GMT — UNRWA tana makokin ma'aikatanta 63 da aka kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba
Hukumar Ayyuka da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta yi makokin ma'aikatanta 63 da aka kashe a Gaza sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai wa tun daga 7 ga watan Oktoba.
"Babu wata kalma da za ta fayyace irin baƙin cikin da muke ciki na kashe ma'aikatanmu na UNRWA 63 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba," kamar yadda UNRWA ta wallafa a shafinta na X.
"Dole ne a yanzu a kawo ƙarshen wannan kashe-kashe da wahalhalun da ake sha a kullum," hukumar ta ƙara da cewa.
Ta ce duk da dumbin barazanar da ma'aikatanta ke fuskanta, UNRWA za ta ci gaba da yi wa mutanen da ke cikin buƙata hidima a Gaza.
UNRWA ita ce babbar hukumar MDD da ke aiki a Gaza.